PDP Ta Yanke Shawarar Tsayar Da Dan Arewa A 2023------Babangida

PDP Ta Yanke Shawarar Tsayar Da Dan Arewa A 2023------Babangida

Dakta Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja, ya bayyana matsayin jam'iyyar PDP kan yankin da za ta mika tikitin takarar shugaban kasarta a zaben 2023.
Tsohon Gwamnan ya ce jam'iyar adawar ta yanke shawarar bayar da takarar shugaban kasar a yankin Arewa, sai dai duk da hakan an aminta duk wanda yake  son tsayawa takarar yana iya fitowa a kowane yanki  na Nijeriya.

Babangidaan ya furta hakan ne a lokacin da kungiyar neman goyon bayan Atiku suka ziyarce shi in da ya furta zai goya masu baya kuma yana da yakinin su ne za su yi nasara.
"A yarjejeniyar ta shiyya-shiyya, mun yanke shawarar sake mika tikitin ga Arewa kamar yadda saura suka bukata amma mun yarda a rubuta a bayyane sakamakon abun da ya faru cewa duk dan takara daga kowane yankin kasar na iya takarar wannan zabe."
Ya bawa Kungiyar ga wannan namijin kokarin da ta yi na shiga lungu da sakon Nijeriya domin tabbatar da nasarar Atiku Abubakar ya zama dan takara a jam'iyar PDP.