PDP Ta Taya Al'ummar Musulmi Murnar Fara Azumin  Ramadan

PDP Ta Taya Al'ummar Musulmi Murnar Fara Azumin  Ramadan

 

Jam'iyar PDP reshen jihar Sakkwato ta taya al'ummar musulmi murnar fara Azumin watan Ramadana na shekarar 1443 wanda ya yi daidai da 2022 dafar a yi lafiya a kare lafiya.

Shugaban jam'iyar  Honabul  Bello Aliyu Goronyo ya kuma yi godiya ga Gwamnatin jihar Sakkwato  karkashin jagorancin Aminu waziri Tambuwal  kan  ba da dama a cigaba shirin ciyar da  abinci ga al'umma a cikin wannan wata na Ramadan 'duk da rashin  kudi da Gwamnati ke fuskanta bai bari aka fasa ba wanan abin yabawa ne muna fatar wannan kwamiti ya rike amanar da aka ba su,' a cewar Bello Goronyo. 

 
A bayanin da jami'in hulda da jama'a na jam'iyar Honarabul Abdullahi Yusuf Hausawa ya baiwa Managarciya a Assabar ya ce  jam'iyar PDP tana sanarda al'umma Sakkwato  cewa ta rage lokacin aikin Ofis nata daga karfe 8 na safe zuwa 4 na yamma duba da yanda hidikwatar take kusa ga in da ake gudanar da tafsirin Azumin watan Ramadan domin a samu damar gudanar da  karatu cikin sauki da natsuwa  

 
Shugaba Bello Goronyo ya yi  fatar malamai da sauran al'umma su yi umfani da wanan damar ga yin  addu'ar samun zaman lafiya a Sakkwato da kasa  baki daya, 'Allah ya kaddari a yi zaben 2023 lafiya a kare lafiya' 
 
'Haka ma muna godiya da irin goyon bayan da ake baiwa Gwamnati da jam'iyar PDP a jiha da kasa baki daya', Kalaman Bello Goronyo.