PDP ta shawarci Gwamnan Sakkwato Kan Yadda Yake Kashe Kudin Jiha

PDP ta shawarci Gwamnan Sakkwato Kan Yadda Yake Kashe Kudin Jiha

Shugaban jami’iyar PDP matakin jihar Sakkwaato Alhaji Bello Aliyu Goronyo  ya shawarci gwamnan jiha Dakta Ahmad Aliyu Sokoto kan yadda yake kashe kudin jihar ba tare da la’akari da bukatar al’umma ba.

Shugaban a wurin zaben shugabanni na jiha da aka gudanar ya ce gwamnan na kahe biliyoyin kudi a wurin gyaran bohol  da sanya raga a saman titi a lokacin da aka fita batun harkar ilmi da kiyon lafiya.

Shugaba Bello Goronyo ya nuna rashin gamsuwarsa da yadda gwamnatin Sakkwato ke tafiya kan haka ya yi wa magoya bayan PDP albishir kan za su samu nasara a zaben 2027 dake tafe.

PDP ta zabi sabbin shugabannin jam'iyar 39 da za su ja ragamar jam'iya  in da Bello Aliyu Goronyo ne shugaba da mataimakinsa Aliyu FC da sakataren jam'iya Abubakar Bashire da Ma'ajin jam'iya Yahaya Ibrahim.

Sai jami'in hulda da jama'a Hassan Sahabi da shugabar mata Zainab Bashir, da sauransu.