PDP Ta Naɗa Tsohon Ministan Sufuri Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Gwamnan Sakkwato

PDP Ta Naɗa Tsohon Ministan Sufuri Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Gwamnan Sakkwato
Shugaban jam'iyar PDP na jihar Sakkwato Alhaji Bello Aliyu Goronyo ya sanar da mukaman kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamnan Sakkwato a 2023.
Ya sanar da sunayen ne a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyar a Kasarawa.
Goronyo ya ce an yi tsarin kamfen kansil ne Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne Shugaba, sai Malam Sa'idu Umar Ubandoma dan takarar Gwamna zai zama mataimakinsa. 
Ya ce tsarin mata da matasa da 'yan kasuwa da malamai na ciki domin a tafi da kowa.
Ya ce  Babban daraktan Kamfe a jihar Yusuf Suleiman tsohon ministan sufurin Nijeriya, mataimaki a yaɗa labarai Saleh Mamman.
Daraktan a wurin jawabinsa ya ce sun karɓi wannan aikin kuma za a samu nasara da ikon Allah.
"lokaci ne da yakamata mutane su nunawa duniya su ke zaɓe, kan haka ba za a mu bari ko kujera ɗaya ta bar PDP ba a zaɓen 2023.
"za a tabbatar da wannan jiha ta PDP ce da ikon Allah, mun shirya cin zaɓe ba da fitina". A cewarsa.