Managarciya

PDP ta lashe gaba ɗaya kujerun ciyamomi da na kansiloli a zaɓen ƙananan hukumomi a Osun

Jam’iyyar PDP ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi 30 da na kansiloli 332 a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jiya Asabar a Osun.

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar, OSSIEC, Hashim Abioye, ne ya sanar da sakamakon zaben a gidan talabijin mallakin gwamnati, Osun Broadcasting Corporation, OSBC, a Osogbo.

Mista Abioye ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa 18 ne suka shiga zaben amma PDP ta lashe dukkan kujerun.

Ya kuma ce an yi zaɓen bisa bin doka da ka’ida.

Exit mobile version