PDP Ta karɓi Shugabannin  Mazaɓar Ministan 'Yan Sandan Nijeriya a Sakkwato

PDP Ta karɓi Shugabannin  Mazaɓar Ministan 'Yan Sandan Nijeriya a Sakkwato
Daga cikin wadanda suka canza Shekar, sun hada da Sakatare jam'iyar APC na Mazabar Dingyadi Badawa,  Ummaru Hassan da mataimakin ma'aji Manu Abubakar da PRO Abubakar Namakka, da Alh Borno Akamawa da Kuma wasu mutum 4 da dukkanin su delicates wato masu zaben dantakara a cikin jam'iyar APC.
Da yake gabatarda wadanda suka canza Shekar, kwamishinan filaye da gidaje Hon Aminu Bala Bodinga, yace, sun canza Shekar ne bisa gansuwa da salon mulkin gwanna Àminu Waziri Tambuwal.
Da yake magana a madadin wadanda suka canza Shekar, tsohon sakataren jam'iyar APC a Mazabar Dingyadi Badawa, Ummaru Hassan, yace sun gansu da salon mulkin jam'iyar PDP a jahar a jahar Sokoto,Kuma sun gansu su hada Kai da gwannatin jahar Sokoto domin ciyarda jahar nan gaba.
Ya Kuma yi bayanin cewa, jam'iyar APC wadda suka zaba, ta kasa ta Kuma baiwa 'yan Najeriya kunya, a kowane mataki.
Suyi alkawalin Bada cikakken goyon baya ga jam'iyar PDP  Kuma zasu jefa kuri'un su ga 'yan takarar jam'iyar PDP a zabe Mai zuwa 
Da yake karbar wadanda suka canza Shekar, shugaban jam'iyar PDP na jahar Sokoto Hon Bello Aliyu Goronyo, ya basu tabbacin cewa, yanzu sun zama 'yan jam'iyar PDP kamar kowa, 
Yayi alkawalin daukar su tankar kowane dan PDP sannan yayi kira garesu dasu yi amfani da kwarewarsu wajen ganin samun nasarar jam'iyar PDP.
 
Za a iya cewa PDP ta yi babban kamu a mazaɓar ministan 'yan sandan Nijeriya kenan ganin ta raba shi da waɗan nan shugabanni.