PDP Ta Jingine Karba-Karba Ta Aminta Atiku Da Tambuwal Da Kwankwaso Su Fito Takara

PDP Ta Jingine Karba-Karba Ta Aminta Atiku Da Tambuwal Da Kwankwaso Su Fito Takara

Jam'iyar PDP mai adawa a Nijeriya ta bude kofarta tare da bayar da dama ga duk wanda yake son tsayawa takarar shugaban kasa da ya fito a kowane yanki yake a 2023.

Wannan matakin zai baiwa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da tsohon shugaban majalisar dattijai Sanata Bukola Saraki da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da sauransu  damar shiga takarar neman samun tikitin tsayawa shugaban kasa a jam'iyar PDP.

A hirar da jaridar PUNCH ta yi da sakataren yada labaran PDP Mista Debo Ologunagba ya  ce jam'iyarsu ba ta hana kowa shiga zabe ba, saboda shekarru ko don ya fito a wani bangare.

Ya ce dole su tseratar da kasar nan a halin da take a yanzu, in har suna son haka ta faru ba ruwansu da in da shugaban kasa zai fito, iyawa da kwarewa da mutunci su ne za su yi aiki.

Ya ce a PDP mutum a kowane bangare ya fito zai iya tsayawa takara, kawai abin da za a yi a tabbatar da an yi sahhihi ingantaccen zaben fitar da gwani, ba ruwanmu da karba-karba kan wanda zai yi wa jam'iyarmu takara.

"Kowane mutum ya cancanta ya fito don yana da damar da zai tsaya takara, ba wanda za a dakatar da shi, muna tafiya ne da tsarin jamiya da kundin tsarin mulkin kasa." a cewarsa.