PDP Ta Dakatar da Tsohon Gwamna a Arewa, Ta Kawo  Dalilai 

PDP Ta Dakatar da Tsohon Gwamna a Arewa, Ta Kawo  Dalilai 

 

Jam'iyyar PDP a jihar Benue ta dakatar da tsohon gwamnan jihar, Samuel Ortom. 

Jam'iyyar ta dauki mataki ne saboda zargin Ortom da yi mata zagon kasa yayin taron jam'iyyar da aka yi.
TheCable ta tattaro cewa PDP na zargin Ortom da kawo rudani yayin taron jam'iyyar na unguwanni da kuma satar kayayyakin zabe. 
PDP ta ce halayyar Ortom ta cin dunduniyar jam'iyyar ta hana samun damar gudanar da tarurruka a kananan hukumomin jihar da dama. 
An dakatar da Ortom ne har na tsawon wata daya tare da wasu mutane guda uku da ake zarginsu tare, cewar Punch. 
Sakataren jam'iyyar a jihar, Joseph Nyam shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a jiya Litinin 5 ga watan Agustan 2024. 
"Yayin gudanar da tarurrukan jam'iyyar PDP a ranar 27 ga watan Yulin 2024 a unguwanni 276, ka kawo rudani wurin goyon bayan satar kayayyakin zabe."