PDP: Shugabannin rikon ƙwarya a jihar Zamfara sun kama aiki
Shugabannin gudanarwar jamíyar PDP na kasa bisa ga tanadin doka sashe na 29(2)(b) a kundin dokar PDP wanda aka yi wa gyaran fuska 2017 sun nada kwamitin rikon kwarya da zai kula da tafiyar da jam’iyar PDP a jihar Zamfara.
A bayanin da sakataren yada labarai na jam’iyar PDP na kasa Kola Ologbodiyan ya fitar ga manema labarai ya bayyana sunayen shugabannin rikon kwaryar su 10, in da aka ba su wa’adin kwana 90 domin gudanar da zaben sabbin shugabanni.
Shugaban jam’iyar a jiha Honarabul Umar Bature, sai Yusuf L. Dambazzau matsayin Sakatare da Farouk Shettima Rijiya Mamba da Alhaji Barmo Abdullahi Kanoma Mamba
da Alhaji Muhammadu Dan Gwamna Gummi Mamba.
Sauran sun hada da Alhaji Usamatu Maharazu Marafa -Mamba da Bala Mohammed Zurmi Mamba da Sani Ahmed Kaura Memba da shugabar mata Medinah Shehu da shugaban matasa Abba Bello Oando.
A karshe uwar jam’iyar ta nemi masu ruwa da tsaki su hada kansu a Zamfara domin samun nasarar kujerarsu da aka kwace masu.
Shugabannin sun soma aiki da fara zagayen sakatariyar jam’iya don ganin halin da take ciki.




