PDP: Shugabannin rikon ƙwarya a jihar Zamfara sun kama aiki

PDP: Shugabannin rikon ƙwarya a jihar Zamfara sun kama aiki
PDP: Shugabannin rikon ƙwarya a jihar Zamfara sun kama aiki
Shugabannin gudanarwar jamíyar PDP na kasa bisa ga tanadin doka sashe na 29(2)(b) a kundin dokar PDP wanda aka yi wa gyaran fuska 2017 sun nada kwamitin rikon kwarya da zai kula da tafiyar da jam'iyar PDP a jihar Zamfara.
A bayanin da sakataren yada labarai na jam'iyar PDP na kasa Kola Ologbodiyan ya fitar ga manema labarai ya bayyana sunayen shugabannin rikon kwaryar su 10, in da aka ba su wa'adin kwana 90 domin gudanar da zaben sabbin shugabanni.
Shugaban jam'iyar a jiha Honarabul  Umar Bature, sai Yusuf L. Dambazzau  matsayin Sakatare da  Farouk Shettima Rijiya Mamba da Alhaji  Barmo Abdullahi Kanoma  Mamba
da Alhaji  Muhammadu Dan Gwamna Gummi Mamba.
 
Sauran sun hada da  Alhaji  Usamatu Maharazu Marafa -Mamba da  Bala Mohammed Zurmi Mamba da Sani Ahmed Kaura Memba da  shugabar mata Medinah Shehu da shugaban matasa  Abba Bello Oando.
 A karshe uwar jam'iyar ta nemi masu ruwa da tsaki su hada kansu a Zamfara domin samun nasarar kujerarsu da aka kwace masu.
Shugabannin sun soma aiki da fara zagayen sakatariyar jam'iya don ganin halin da take ciki.