PDP Da APC Ba Su Goyon Bayan Takarar Mata A Cikin Jam’iyyun---Aisha Aliyu Gusau
"Bana sha’awar sake fitowa takara don duk manyan jam'iyyun APC da PDP ba su da lafiyar da za a fito takara cikinsu, kuma ba su goyon bayan takarar mata a hakikanin gaskiya".
"Bana sha’awar sake fitowa takara don duk manyan jam'iyyun APC da PDP ba su da lafiyar da za a fito takara cikinsu, kuma ba su goyon bayan takarar mata a hakikanin gaskiya".
Hajiya Aisha Garba Aliyu Gusau ce ta yi wannan furucin a zantawarta da mujallar Managarciya a satin da ya gabata domin sanin in da alkiblar siyasarta ta sa gaba, ganin cewa ita sanannar 'yar siyasa ce Arewa da kasa baki daya.
Ta ce har Yanzu ita 'yar jam'iyar PDP ce tana cikin jam’iyar, amma maganar takarar ce ta janye a yanzu, don ko bayan matsalar jam'iyyun, akwai ta babakere da maza ke musu, su hana masu rawar gaban hantsi, abin da ke ci wa mata tuwo a kwarya.
"A shekarar 2005 na shiga siyasa na fito neman 'yar majalisar jiha a Gusau ta tsakiya, a zaben fitar da gwani dattawan jam'iya suka roke ni da na janye, ba yanda na iya dole na hakura da neman kujerar, wannan lamari na ci wa mata tuwo a kwarya.
"Wani abu daban bayan babakeren da ake yiwa mata a cikin tsarin jam'iyya, akwai rashin hadin kai a wurin 'yan uwansu mata, ba su ba da hadin kai su zabi mace, in da maza suka karkata nan suke tafiya, da za mu samu hadin kan mata a kasar nan da za a samu mata a mukaman zabe fiye da yanda ake yau." Hajiya Aisha Gusau.
Ta kara da cewar ta yi shugabar mata ta PDP a kasa baki daya, bayan shugabar mata ta Arewa a kungiyar neman dawo da mulkin Nijeriya a Arewa, wadda Sola Saraki baban tsohon shugaban majalisar Dattawa Sanata Bukola ya kafa, duk wannan gogewar bai hana aka kira ni da ni ba 'yar jiha ba ce, jihar da na fi shekara 30 cikinta. Ka gani mata na fuskantar tirjiya a siyasar Arewa.
managarciya