Home Rahoto Obi yana jagorancin masu zanga-zanga zuwa Majalisar Ƙasa kan yada sakamakon zaɓe...

Obi yana jagorancin masu zanga-zanga zuwa Majalisar Ƙasa kan yada sakamakon zaɓe kai tsaye

5
0

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam’iyyar LP, Peter Obi, ya jagoranci jerin masu zanga-zanga zuwa harabar Majalisar Ƙasa da ke Abuja domin nuna rashin amincewa da yadda ake tafiyar da batun yada sakamakon zaɓe kai tsaye ta hanyar na’ura.

Masu zanga-zangar sun buƙaci ‘yan majalisa su tabbatar an tanadi doka mai ƙarfi da za ta wajabta a rika watsa sakamakon zaɓe a ainihin lokacin da aka kammala ƙidaya a rumfunan zaɓe, suna mai cewa hakan ne kawai zai ƙara gaskiya, amincewa da kuma kare ƙuri’un al’umma.

Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan gyaran dokokin zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda batun amfani da fasaha wajen watsa sakamako ya zama jigon cece-kuce tsakanin ‘yan siyasa da kungiyoyin farar hula.

Masu lura da al’amuran siyasa na ganin wannan mataki na iya ƙara zafafa muhawara kan sahihancin zaɓe da kuma yadda za a tabbatar da adalci a zabe mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here