NLC ta buƙaci gwamnatin taraiya da ta fasa shirin ta na karin albashin masu mulki 

NLC ta buƙaci gwamnatin taraiya da ta fasa shirin ta na karin albashin masu mulki 

 

Kungiyar kwadago ta ƙasa, NLC, ta to kira ga Hukumar tattara kudaden shiga da kasafin kudi, RMAFC, da ta dakata da shirin karon albashi ga masu madafun iko.

Shugaban RMAFC, Mohammed Shehu a kwanakin baya ya baiyana cewa shugaba Bola Tinubu na ɗaukar Naira miliyan 1.5 a matsayin albashi kuma ministoci na ɗaukar ƙasa da Naira miliyan 1 kuma ya ce haka yake tun 2018.

Shehu ya kara da cewa hakan bai dace ba kuma sai an yi duba akai an kawo gyara.

Sai dai shugaban NLC na kasa, Joe Ajero ya ce wannan shirin bai kamata ba kuma rashin adalci ne da tausayi ga yan Nijeriya .

A cewar Ajero, tsarin wani mataki ne na kara fadada gibin dake tsakanin masu mulki da talakawa.

Ajero ya shawarci RMAFC da ta dakata da shirin Sannan a kauna albashin da kowanne mai rike da madafun iko ke dauka.