Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya ce Najeriya ta kunyata kanta da kuma Afrika baki daya. Ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi wajen kaddamar da wani littafi da tsohon ministan masana'antu da zuba hannun jari, Olusegun Aganga ya rubuta kamar yadda The Punch ta wallafa.
Obasanjo ya ce Najeriya ta gaza cimma muradunta tun bayan samun 'yancinta shekaru 63 da suka gabata, inda ya ce ta kunyata Afrika ma ba iya kanta kadai ba.
Shugaba Tinubu ne ya kaddamar da littafin ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan tsare-tsaren harkokin kudi, Olawale Edun. Taron ya samu halartar manyan Najeriya da dama da suka kunshi tsofaffin shugabanni da masu ci a yanzu.
Obasanjo wanda ya halarci taron ta manhajar taro ta zamani, ya bayar da muhimman shawarwarin da za su taimaka kasar ta ci gaba.
Daga cikin abubuwan da ya yi magana a kansu akwai maganar tsaro da zaman lafiya, wadanda ya ce ba za a iya samunsu ba har sai an tabbatar da adalci a kasa. Haka nan ya ce barin sama da yara miliyan 20 na gararamba a kan titi ba tare da zuwa makaranta ba kalubale ne babba da ya zama dole a magance shi in ana so a ci gaba.