Ni zan kammala aikin wutar Mambila idan na ci zaɓe -- Tinubu
Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin kammala aikin wutar lantarki na Mambila da ya ƙi ci ya ƙi cinye wa.
Tinubu ya kuma yi alƙawarin shawo kan matsaloli da ke arewacin Nijeriya ke fuskanta da kuma kasar baki daya muddin ya zama shugaban kasa.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi a wani taro da kungiyoyi masu fada aji na arewacin Najeriya da suka hada da kungiyar dattawan arewa da kuma Arewa Consultative Forum suka shiryawa 'yan takarar shugaban kasa a Arewa House, a JIhar Kaduna.
Tinubu ya ce cikin abubuwan da zai fara yi shine kammala aikin wutar Mambilla da aka shafe tsawon shekaru ba tare da yin aikin ba, inda ya ce tashar za ta samar wa da kasar wuta mai karfin megawatt 3,050 da kuma zai kasance daya daga cikin tasha mafi girma a fadin kasar.
“Abin da yake kawo jinkirin kammala wannan aikin shine rashin isassun kudade. Ba ma kebe isassun kudade wa manyan ayyuka masu daukar dogon lokaci. Za mu kammala wadannan aiki saboda muna zuwa da wani tsari mai kyau ga kasar,'' in ji Tinubu.
Ya kuma ce zai kawo masu zuba jari a ciki da kuma wajen kasar wadanda za su kammala aikin da kuma zai kawo wa kasar ci gaba.
managarciya