Ni ba mai fada da cikawa ba ne----Gwamnan Sakkwato
Gwamnan jihar Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu ya musanya maganar da ake yi kansa cewa shi Gwamna ne mai fada da cikawa.
Gwamnan Sakkwato ya yi wannan kalamin ne a wurin taron ziyarar godiya da ya kai a karamar hukumar Dange Shuni ya ce ba dai dai ba ne a ce masa mai fada da cikawa kuskure ne, fada ce yake yi cikawa ta Allah ce.
Managarciya ta fahimci sakataren yada labaran Gwamna Abubakar Bawa ne ya yi masa kirari a lokacin da ya gayyato shi don jawabi ya ce Gwamna mai fada da cikawa, “ina son na yi gyara kan maganar da ake cewa Gwamna mai fada da cikwa, wannan magana ba haka take ba kuma ba daidai take ba, kuma ba daidai ba ne, matsayina na Gwamna nakan fada Allah ke cikawa," kalaman Gwamnan Sakkwato.
managarciya