NDLEA ta kama mutane da miyagun ƙwayoyi a jihohin Kano, Lahadi, Kwara da Ribas
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kama wasu manyan mutane da kuma kama miyagun kwayoyi a fadin jihohin Legas, Kwara, Kano, da Ribas.
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi.
A cewar sanarwar, a ranar 1 ga Janairu, 2025, jami’an NDLEA sun kama wata mata mai suna Alhaja Aishat Feyisara Ajoke Elediye, mai shekara 61, wacce aka fi sani da “Iya Ruka,” a gidanta da ke Okota, Legas.
Ta kasance cikin jerin mutanen da hukumar ke nema ruwa a jallo domin jagorantar wata babbar kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi a Mushin.
Kame ta ya biyo bayan kama wata babbar mota dauke da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 1,540, wanda ma’aikacinta Abideen Adio ke tukawa. Alhaja Ajoke, wacce ta fito a matsayin ’yar kasuwa da ke shigo da yadudduka da takalma, ta kasance mai son jama’a kuma shugabar kungiyar mata ta Legas.
Daga Abbakar Aleeyu Anache
managarciya