Nan Gaba Kadan Za a Magance Matsalar Tsaro a Sokoto---Yusha'u Kebbe
Shugaban kwamitin samar da rundunar tsaro a jihar Sakkwato Alhaji Yusha'u Ahmad Muhammad Kebbe ya kara tabbatar da za a samu tsaro a jihar Sakkwato nan gaba kadan ganin yadda Gwamnatin Dakta Ahmad Aliyu ta tashi tsaye don Magance matsalar tsaro a jihar.
Yusha'u Kebbe a zantawarsa da manema labarai a Sokoto ya ce a lokacin da mai girma Gwamna ya yanke shawarar kafa rundunar tsaro ta a al’umma a jihar Sakkwato wasu mutane ba su fahimce shi ba, wasu kuma suka siyasantar da maganar suna ganin ba da gaske ake yi ba, kwamitin da aka kafa bata lokaci ne kawai. Sanya hannu a dokar da Gwamna ya yi ya sa an gane duk masu sukar dokar suna fadin son rai ne kawai, a maganar da nake da kai ana kan tantance wadanda za a dauka aikin na samar da tsaro, da zaran an kammala wadan da suka yi nasara za su fara karbar horo don su samu Kwarewa ga abin da aka sanya gaba na samar da tsaro a jiha.
"Rundunar tsaron kamar yadda Mai girma Gwamna ya fada ba kishiyoyin jami'an tsaro ba ne sai dai an yi su ne don su tallafa ga samar da zaman lafiya, kuma za su yi aiki ne kafada-kafada da jami'an tsaro ba tare da sabawa tsari da doka ba.
"A zagayen da muka yi a kananan hukumomi jiha mun fahimci da yawan wadan da ke son shiga aikin suna harkar banga ko kungiyar samarda tsaro ta yankin da suke, suna taimakawa jami'an tsaro a wurin gudanar da aiki, ka ga kenan gwamnati ba ta zo da wani abu sabo ba sai dai ta mayar da abin a hukumance ne don abin ya tafi cikin tsari don cimma manufar da ake bukata."
Shugaban ya ce yakar 'yan bindiga ya sauya salo domin a yanzu jami'an tsaro ba su jiran sai an kai hari sannan su farmaki 'yan bindiga, a halin da ake ciki sukan bi su har maboyarsu, hakan zai taimaka sosai wurin wanzar da zaman lafiya, wannan gwamnati na ganin jami'an tsaron da ake da su ba su isa in aka samu tallafin a kalla mutum 2000 da za a dauka cikin karamin lokaci ana iya shawo kan matsalar tsaron jiha, nan gaba kadan za a magance matsalar tsaro a Sokoto.
managarciya