Nan Ba da jimawa Ba Za a Magance Matsalar Tsaron Da Ke Addabar Nijeriya-----Sanata Wamakko

Tsohon Gwamnan na Sakkwato  ya yi bayanin cewa nan ba da jimawa ba kasar nan za ta fita cikin kalubalen da take fama da shi, kasancewar Hukumomin tsaro na bangarori da dama a kasar nan suna iya kokarin su na ganin an kawo karshen wannan matsalar.

Nan Ba da jimawa Ba Za a Magance Matsalar Tsaron Da Ke Addabar Nijeriya-----Sanata Wamakko
Nan Ba da jimawa Ba Za a Magance Matsalar Tsaron Da Ke Addabar Nijeriya-----Sanata Wamakko

Shugaban kwamitin tsaro na Majalisar Dattawa ta kasa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana kwarin gwiwar sa nan gaba kadan matsalar tsaron da ke addabar kasar nan zai Zama tarihi da yardar Allah.

Sanata Wamakko Mai wakiltar Gundumar Sakkwato ta Arewa ya bayyana hakan ne a Gidansa dake Gawon Nama a birnin Sakkwato yau Assabar Jim kadan bayan da ya dawo daga  ziyarar aiki a Abuja.

Tsohon Gwamnan na Sakkwato  ya yi bayanin cewa nan ba da jimawa ba kasar nan za ta fita cikin kalubalen da take fama da shi, kasancewar Hukumomin tsaro na bangarori da dama a kasar nan suna iya kokarin su na ganin an kawo karshen wannan matsalar.
 
Sanata Wamakko a bayanin da Bashar Abubakar MC, Mataimaki na Musamman gare shi kan kafar sadarwa  ta zamani ya ce shugaban kasa Buhari ya ba da  dukkan goyon bayan da ya Kamata ga hukumomin tsaro da zimmar tunkarar kalubalen dake dabaibaye a kasar nan.
 
 Ya bayyana sha'anin Yan Bindinga da Masu garkuwa da Jama'a da cewa abin damuwa ne, Inda ya ce mafita guda kawai ita ce a kama addu'a domin samun kai karshen wannan matsalar.
 
Ya roki Allah madaukakin sarki da ya tsaga zuciyar wadannan mafitinan da su tuba su daina wannan bakar tabi'ar.
 
A karshe  ya taya murna ga 'yan Nijeriya kan cikar shekara 61, kana ya  waiwayi irin ci gaban da aka samu a bangaren shimfida tituna, Samar da ruwan sha  da hasken lantarki Hadi da raya al'umma.