Naira Ta Yi Faɗuwa Mafi Muni Bayan Sanar Da Shirin Sauya Fasalin Kuɗin Najeriya

Naira Ta Yi Faɗuwa Mafi Muni Bayan Sanar Da Shirin Sauya Fasalin Kuɗin Najeriya

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Farashin takardar kudi ta dalar Amurka a Najeriya ya kai kololuwa a kasuwannin musayar kudaden ketare a Najeriya inda a safiyar yau talata aka rika sauya duk dala daya kan Naira 815 zuwa 818, lamarin da ke nuna wadda kudin na Najeriya ke cigaba da rasa daraja,

Wani bincike ya nuna cewa tun bayan yunkurin babban bankin kasar CBN na sauya fasalin wasu daga cikin takardar kudin Najeriya ne aka fara ganin rububin sayen takardar kudin ta dala a kasuwanni wanda bayanai ke cewa mutanen da ke makare da kudi a ajje suke saurin sayen dalar don kaucewa fuskantar asara, 

Kasuwannin musaya na bayan fage dai a yau talata sun wayi gari da karancin dala baki daya lamarin da ya sa rashin daidaituwar farashin kudin na Amurka dai dai lokacin da sabbin Kudin Najeriya ke shirin fitowa a ranar 15 ga watan Disamba mai zuwa,

A makon jiya ne CBN ya sanar da sake faduwar darajar Naira zuwa 765 kan duk dala guda wanda ke nuna faduwar Naira 53 cikin kwanaki 5 mafi kololuwar koma baya da Najeriya ta taba gani a tarihi.