A cewarsa masu sayarda kayan in aka kama su sai su rika fadin ba su San kayan abincin sun lalace ba domin ba su duba kwanan watan kayan balle su san wa’adin da aka diba na amfani da su ba, a hakan za su shigo da kayan abinci da ya gurbata ko yake kusa da lalacewa a rika sayarwa mutane a shaguna da kasuwa.
Garba Adamu ya ce wanda hukumar ta kama za a hukunta shi, bayan karbe Magin da aka yi domin ya zama guba bai kamata mutane su yi amfani da su ba.
Ya yi kira ga mutanen Nijeriya a koyaushe su rika duba rijistar NAFDAC da Kuma kwanan watan da Kamfani ya dibarma kayan a yi amfani da su kafin su saye ko su yi amfani da su.
Adamu ya godewa jami’an tsaron da ke taimakawa hukumar da kungiyoyin ‘yan kasuwa na jiha da daidaikun mutane da kungiyoyin cigaba da ke taimakawa NAFDAC domin tsare lafiyar al’umma.
“Wasu ‘yan kasuwa nada halin kawo kayan da suka gurbace ko suka yi kusan lalacewa a kasuwar Sakkwato da wajenta, wasu Kuma a tafi da su a kasuwannin Boda da kauyukka domin a sayar da su,” a cewarsa.
Kodineta ya gargadi masu sayarda kayan da suka gurbata ko suka lalace da wadanda ba su da rijistar NAFDAC masu yin haka doka za ta yi aikinta kansu a kowane lokaci aka samu nasarar damke su.





