Muyi amfani da Social media dan neman Aljanna------Mufti menk

Muyi amfani da Social media dan neman Aljanna------Mufti menk
Sheikh Mufti Menk


Daga Mukhtar Haliru Haliru Tambuwal Sokoto.  
Babban malamin nan na Duniya kuma maifatawa a kasar Zimbabwe,  Sheikh Ismail Mufti Menk, ya gabatar da kasida mai taken karfafa Shaanin hadin kai, zaman lafiya da cigaba a Najeriya da Afirika ta Yamma.
Darussa daga Rayuwar Sheikh Usmanu Dan Fodiyo Wanda aka soma tun ran lahadi 24 ga watan goma za a kare larba 4 ga qa Nuwanba. 
A lokacin tarukkan an gabatar da kasidu da laccoci daga masana daga garuruwa daban daban, anyi kacici-kacici tsakanin makarantun, da addu'a da sauran karatu.
Babban malamin ya gabatar da kasidar sa a yau Talata, ya bayyana cewa kafar sadarwar ta zamani kowa na iya amfani da shi da yadda ya dace ta yadda zai iya bidar wut ko Aljanna,kuma mu sani duk abin da mukayi zaayi muna hisabi a gobe kiyama
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal yayi godiya kan wannan taron inda ya bayyana ba da tallafi naira miliyan 20 daga Gwamnatinsa, kashin kansa, da  gwamnonin kebbi da Zamfara. 
 Sarkin Musulmi ya bayyana cewa dukkkan nasarar da ake fadin an samu nasara ce da aka samu akan kowa da kowa, daga nan ya ayyana baiwa wasu iyalai da mutane guda biyar da ya zabo ya basu lambar yabo ta lallafin kudi na Naira miliyan biyar ,akan irin gudun mawar da suka bada ta ilimi, zaman lafiya da cigaban daular.  
Taron Wanda hakadar kungiyoyin addinin musulunci a sokoto suka shirya karkashi NACOMYO reshen jihar Sokoto, da jagorancin Sadaukin Sakkwato Malam Muhammad Lawal Maidoki.