Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato

Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato

Mutane Tara sun hadu da ajalinsu a sabon hatsarin jirgi da ya  auku da mutanen ƙauyen Zalla Bango a ƙaramar hukumar Sabon Birni ranar Alhamis data gabata a kokarinsu na tsarewa daga harin 'yan bindiga da suka kai masu.

Wani da yake garin ya shaidawa wakilinmu cewa hatsarin ya faru ne bayan sallar Mgrib bayan da jirgin ya yi lodin mutane mata da maza da yara ƙanana da kayansu yana zuwa in da hanyar mota ta yanke saboda ambaliya da ta hada ƙaramar hukumar Sabon Birni  da Goronyo anan ya bugi karamar gada ya tuntsure.

Ya ce ana haka mutane suka kawo dauki an fitar da mutane Tara da  ba rayuwa a cikinsu, wasu sun samu rauni a cikinsu, jirgin ya dauki mutane masu yawa da ban san adadinsu ba.

Hukumar ba da agajin gaggawa a jiha da sauran hukumomi ba su ce komai ba kan lamarin.

Sanata Ibrahim Lamiɗo ɗan majalisar dattijai dake wakiltar yankin Sakkwato ta Gabas ya yi jaje da ta'aziya ga mutanen da suka samu hatsarin jirgin ya kuma yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin inganta harkar tsaro a yankin.

Sanata Lamiɗo ya ce matsalar tsaro na yi wa yankinsa lahani da mayar da su baya a kullum, bai kamata a zuba ido ana kallon mutane na shan baƙar wahala da kuma rasa rayuwa ba.

"Ina kira ga gwamnati ta juyo kan mutanen gabascin Sakkwato a yi abin da ya dace kan harkar tsaro, akwai buƙatar gwamnatin Sakkwato ta gyara hanyar da ta haɗa Sabon Birni da Goronyo domin matslar hanyar na kara jefa mutane cikin matsalar sufuri.

"Aikin gwamnati ne ta samar tsaro da walwalar jama'a amma a wannan gefen yankinmu a kullum ci baya yake samu dole ne mu cigaba da fadawa gwamnati don a yi abin da ya dace a yankinmu," a cewar Sanata Ibrahim Lamiɗo.