Mutum 5 Sun Rasu 42 Sun Yi Rauni Sanadin Ruwa Tare da Iska a Damaturu
Daga Muhammad Maitela.
Ruwan sama tare da iska mai ƙarfi ya jawo asarar rayukan mutum 5 yayin da ƙarin wasu mutum 42 sun samu mabambantan raunuka, baya ga lalata gidaje da dukiyoyin al'umma da ya yi, da yammacin ranar Litinin a birnin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Makaƙon hadarin haɗi da iska mai ƙarfin gaske ya fara da misalin qarfe 5:00 na yammacin ranar, tare da saukar ƙanƙara, al'amarin da ya jawo rushewar wasu gidaje, haɗi da kwashe rufin ɗakunan jama'a da ɓarnata dukiyoyin jama'a a babban birnin.
Da yake tabbatar da varnar da ruwan daman ya yi, Darakta a hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Yobe (SEMA), Malam Baba Jalo ya shaida wa manema labaru cewa mutum 5 ne suka gamu da ajalinsu ta dalilin wannan ibtila'i haxi da qarin wasu mutum 42 da suka samu raunuka a sanadiyar qaqqarfan iskan.
Wasu da dama daga cikin waxanda suka samu raunukan an kwantar dasu a vangaren kula da majinyata na gaggawa na asibitin qwararru da ke Damaturu.
Har wala yau, Malam Jalo ya qara da cewa, ruguzawar gine-gine ne ya jawo mutuwar mutum biyar xin da suka gamu da ajalinsu a qaqqarfan iskan mai haxe da ruwan sama da qanqara.
“Jiya (Talata), mun samu nasarar kwashe jama'ar da suka samu raunukan, wanda adadin su ya kai 42 zuwa xakunan kula da majinyata na gaggawa da ke asibitin qwararrun, sannan baya ga wannan akwai jama'a da dama waxanda suka samu qananan raunuka ta dalilin wannan ibtila'in."
“Haka kuma, al'amarin ya jawo mutuwar mutum biyar, waxanda gidaje suka ruguzo a kansu. Wannan ya faru ne a magidanta uku dake unguwar Abbari Mai Mala a nan birnin Damaturu." Ta bakin Jalo.
Bugu da qari kuma, ya bayyana cewa wuraren qaqqarfan iskan ya varnata kayayyakin jama'a sosai fiye da ko'ina a birnin sune unguwannin Maisadari, Nayinawa, da Pompomari.
Ya ce hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Yobe ta na aiki tuquru wajen gano ta'adin da qaqqarfan iskan ya yi domin xaukar matakan da suka dace.
Baba Jalo ya yi qarin haske da cewa, wannan qaqqarfan iska tare da makaxon hadarin suna da alaqa da sauyin yanayin da duniya ke fuskanta, inda ya ce, “Saboda maimakon iskan ya fito daga vangaren arewaci, ko ya kaxa ta shiyyar gabashi, wanda hakan yar manuniya ce dangane da qalubalen sauyin yanayin duniya ke fuskanta." In ji shi.
A hannu guda kuma, Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya miqa saqon ta'aziyya ga mamatan tare da jajanta wa tare da kai ziyara a asibitin da aka kwantar da waxanda suka samu raunuka ta dalilin ibtila'in. Haka kuma ya bayar da umurnin duba maras lafiyan kyauta da addu'ar samun sauqi cikin gaggawa.
managarciya