Mutum 25 sun rasu 15 na asibiti a wata sabuwar Annoba da ta bulla a Sakkwato

Mutum 25 sun rasu 15 na asibiti a wata sabuwar Annoba da ta bulla a Sakkwato
Wata Annoba ta bula a birnin jihar in da ta yi sanadin rasuwar mutane da dama wanda yawansu zai kai 25, an kwantar da wasu a asibiti.
A unguwar Gidadawa a karamar hukumar Sakkwato ta Arewa ne aka samu bullar cutar wani mazauni unguwar ya ce ba wanda ya san dalilin bullar cutar amma an zargi ruwan famfo ne ya haddasa lamarin abin da ya kawo katse ruwa a unguwar gaba daya daga babban layin ruwa na jiha, ana ganin cutar Kwalara ce aka samu.
Kwamishiniyar lafiya ta jiha Hajiya Asabe Balarabe ta tabbatar da faruwar lamarin in da ta ce mutum 25 ne suka rasu sanadin annobar, an kwantar da mutane 15 a asibiti, lamarin ya faru ne a kananan hukumomi uku, Sakkwato ta Arewa da Silame da Kware.
Kwamishiniyar a zantawar ta da manema labarai a Litinin ta ce ana cigaba da bincikar wadanda aka samu da cutar don sanin ko Kwalara ce da daukar matakin da yakamata.
Asabe ta kara bayyana cewa mutum 1, 160 annobar  ta sama sai dai 25 ne suka samu salwantar rayuwa.
"Mutanenmu sun yi aiki sosai na ganin cutar ba ta watsu a wasu wurare ba."
"Gwamnatin jiha ba ta yi kasa a guiwa ba nan take ta sawo tare da raba magani a kananan hukumomi 18 don tabbatar da an dakile yaduwar cutar," a cewar ta.
Dan majalisa mai wakiltar Sakkwato ta Arewa ta daya a majalisar dokokin jiha Buhari Haliru ya nemi gwamnati ta yi gaggawar daukar mataki kan annobar.
Dan majalisar ya ce Annobar ta yi sanadin  hasarar mutane 7, an kwantar da 95  a karamar asibitin unguwar Bazza dake Kofar Rini da babbar asibiti kwararru ta jiha da ta koyarwa ta Usman Danfodiyo duk mutanen sun fito a yankinsa.
Ya nemi gwamnati ta yi wani abu da gaggawa kar cutar ta bazu a wasu wurare.
Ya roki majalisa ta umarci gwamnatin jiha ta sanya dokar ta baci a kiyon lafiya a yankin a kuma gaggauta yin wani abu kan annobar. Haka ma gwamnati ta rika wayar da kan mutane yanda za su kare kansu ga cirutoci. 
"Gwamnati ta tura karin ma'aikatan lafiya a wuraren zaman da cutar ta bulla. A Kuma bibiyi silar bullar cutar don daukar mataki.