Home Labarai Mutanen Sokoto sun bar gidajensu, suna kwana a daji saboda hare-haren ‘yan...

Mutanen Sokoto sun bar gidajensu, suna kwana a daji saboda hare-haren ‘yan bindiga

4
0

Fassara: GaskiyaCast

Mazauna aƙalla ƙauyuka 21 a Jihar Sokoto sun tsere daga gidajensu bayan yawaitar barazana da hare-haren ƴan bindiga, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da: Gidan Kare, Kaware, Chabi, Dattabi, Janwake, Sha Rana, Darbekami, Gidan Sule, Kuruwa, Mahuta, Dantayawa, Kawala, Bagirbe, Tsattsagi, Katsira, Imasa, Bela, Hura Girke, Galadimmai da Asha Ruwa.

Yawancin mutanen da suka rasa matsugunansu yanzu suna samun mafaka a garin Tureta da kewayenta, inda suke fuskantar mawuyacin hali na rayuwa, ciki har da cunkoso, yunwa da rashin tallafi na asali.

Wani mazaunin yankin ya ce yawancin waɗanda suka tsere suna zama ne a gidajen ƴan uwansu maimakon sansanonin ƴan gudun hijira.

“Yawancin waɗanda suka tsere sun fi son zama a gidajen ƴan uwansu inda za su samu mafaka,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa zuwan waɗannan mutane Tureta ya fara ne kusan kwanaki uku da suka gabata.

“Yanzu kusan kwanaki uku kenan da suka fara shigowa Tureta da yawa,” in ji shi.

Wasu kuma a halin yanzu suna samun mafaka ne a Makarantar Firamare ta Abdulbaki Model da ke Tureta, inda aka ruwaito cewa sama da mutane 1,000 ke kwana a cikin ajujuwa masu cunkoso da dare ba tare da wani tallafin jinƙai ba.

Wani mazaunin ƙauyen Kuruwa ya ce yawaitar hare-hare ne ya tilasta musu barin gidajensu da dukiyoyinsu.

“Ba za mu iya ci gaba da zama a gidajenmu ba. Ƴan bindiga sun kai mana hari sau da dama kafin watan Ramadan. Barin wurin ba abu ne mai sauƙi ba, amma ba mu da wani zaɓi,” in ji shi.

Daga Gidan Kare, wani mazaunin ya ce suna jin ƙarar harbe-harbe kusan kowane dare, wanda ke jefa tsoro a zukatan jama’a.
“Gidajenmu sun zama babu kowa, kuma muna damuwa da lafiyar ƴaƴanmu. Muna fatan gwamnati za ta samar da tsaro,” in ji shi.

Wani dattijo daga ƙauyen Bagirbe ya ce da dama daga cikinsu yanzu suna kwana a Tureta kullum saboda tsoro.
“Yawancinmu yanzu muna Tureta, kuma duk wanda ka gani a nan ba ya rayuwa cikin kwanciyar hankali,” in ji shi.

Wani mazaunin ƙauyen Sha Rana ya bayyana cewa sun tsere ne a yammacin ranar Alhamis bayan samun labarin shirin kai wani babban hari.
“Mun bar gidajenmu da yammacin Yau saboda an sanar da mu cewa ƴan bindiga za su kai hari da yawa. Ba za mu koma ba sai tsaro ya inganta,” in ji shi.

Daga nan sai ya roƙi hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa.
“Don Allah a kawo mana tsaro. Kada ku jira lokacin zaɓe kafin ku zo neman ƙuri’unmu,” ya ƙara da cewa.

Wani mazaunin Kuruwa ya ce maharan kan kashe mutane ba tare da bambanci ba yayin hare-hare.

“Idan sun zo, suna kashe maza, mata, yara har ma da tsofaffi. Wannan ne ya sa muka tsere zuwa Tureta domin ceton rayukanmu,” in ji shi.

Ya kara da cewa wasu daga cikin mazauna da ba su samu damar zuwa Tureta ba suna ɓoyewa ne a daji da daddare domin tsira.
“Waɗanda ba su samu damar zuwa nan ba suna ɓoyewa a daji da dare,” in ji shi.

Wata uwa mai ƴaƴa huɗu daga Gidan Kare ta ce hare-haren da aka riƙa kai musu ne ya jawo mutuwar mutane da dama kafin su tsere.

“‘Yan bindiga sun kashe mutane da yawa kafin mu tsere. Mazajenmu kan koma ƙauyen wani lokaci domin ɗauko wasu kaya da za mu sayar mu samu abinci,” in ji ta.

Wata mai juna biyu daga kauyen Hura Girke ta ce a halin yanzu tana samun mafaka a makarantar firamare cikin mawuyacin hali.

“Lokacin haihuwata ya kusa cikin ƙasa da wata guda, amma ba ni da isasshen abinci. Muna cikin wahala a nan,” in ji ta.

Ta roƙi a ɗauki matakin gaggawa domin su samu damar komawa gidajensu cikin aminci.
“Muna butkatar tsaro domin mu koma gonakinmu mu rayu cikin kwanciyar hankali,” ta ƙara da cewa.

Ƙoƙarin jin ta bakin mai ba Gwamnan Jihar Sokoto shawara kan harkokin tsaro, Kanar Usman Ahmad (mai ritaya), da kakakin rundunar Ƴan sandan jihar, DSP Ahmad Rufai, bai yi nasara ba, domin ba su amsa kira ko saƙonnin da aka aike musu ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Iyalan da suka rasa matsugunansu na ci gaba da fuskantar ƙara taɓarɓarewar yanayin jinƙai yayin da suke kira ga hukumomi da su gaggauta dawo da tsaro a yankunansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here