Mutanen Gari Sun Yi Fito Na Fito da 'Yan Bindiga, Sun Hallaka Miyagu Masu Yawa

Mutanen Gari Sun Yi Fito Na Fito da 'Yan Bindiga, Sun Hallaka Miyagu Masu Yawa


Mutanen gari sun hallaka aƙalla ƴan bindiga 37 a ƙauyen Matusgi a ƙaramar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara. Mutanen sun samu nasarar ne bayan sun yi fito na fito da ƴan bindigan waɗanda suka farmaki ƙauyen da niyyar sace mutane. 
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa ƴan bindigan sun shigo ƙauyen ne a kan babura da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Laraba. 
Majiyar ta ce ba wannan ba ne karo na farko da mutanen ƙauyen suka yi fito na fito da ƴan bindigan, amma shi ne karo na farko da suka yi musu ɓarna mai yawa. 
Ƴan bindigan suna shiga ƙauyen sai suka fara harbi kan mai uwa da wabi domin su firgita mutane. 
Sai dai mutanen sun san da zuwansu inda suka yi shiri na musamman kafin su iso. 
Bayan kwashe awa ɗaya ana musayar wuta, ƴan bindigan sun ja da baya bayan an kashe musu mutum 10. 
Daga nan sai mutanen suka sake taruwa suka yi musu kwanton ɓauna. 
Managarciya ta fahimci akwai bukatar gwamnatin jihar Zamfara ta kara karfafa mutanen garin tare da yaba namijin kokarin da suka yi domin haskaka abin da sun ka yi abu ne da ake bukata a sauran wurare domin magance wannan matsalar ta 'yan bindiga ko kuma a rage mata kaifi sosai.