Mutane 'yan gudun hijira da suka fito sama da kauyukka 10 a karamar hukumar Shagari sun rufe hanyar Shagari zuwa Sakkwato domin nuna fushinsu ga gwamnati kan azabar da suke sha hannun 'yan bindiga a yankinsu.
Mutane mata da maza sun mamaye karamar hukumar Shagari don neman daukin gwamnati kan abin da ke addabar su, sun rufe babbar hanyar da ta hada Sakkwato da Kebbi da Neja.
A wannan lahadi da suke zanga-zanga wani daga kauyen Rinaye ya yi magana da Aminiya ya ce "rashin kulawar da gwamnati ta nuna mana ya sa muka rufe hanyar mota don janyo hankalin gwamnati da jami'an tsaro gare mu a dauki matakin kora mana 'yan bindigar su bar yankinmu, yau(Lahadi) sun jera kwana uku kullum sai sun zo sun sace mana mutane kuma ba wasu jami'an tsaro da aka kawo mana don kare mu."
Ya ce 'yan bindigar sun shafe kwana uku a jere suna addabar mutanen kauyukkan a farkon sun tashi kauyukka uku a ranar Juma'a, sun tafi na biyu dana uku a ranar Assabar da Lahadi.
"A garin Rinaye sun sace mai garinmu da dukan limaman garin bayan sun kashe mutum uku sun yi garkuwa da wasu mutanen garin da ba a tantance yawansu ba, a wannan Assabar da Lahadi.
"Shekaran jiya sun shiga garin Aske dodo da Tungar barke da Jandutse duk wadannan wurare babu mutane a cikinsu yanzu sun kashe mutane biyu da yin garkuwa da mutane 15," a cewar majiyar.
Ya ce hukumomin tsaro da gwamnati ba a abin da suka yi a yanzu ko jaje ba a kai musu ba.
Malama Tunba mai yara biyar mata uku da maza biyu da ta fito a kauyen Jandutse ta ce yanzu haka ba ta san in da ɗiyanta suke ba tun da suka gudu a ranar Assabar, a haka ta yini ba abin da ta sa a bakinta.
Tumba ta yi kira ga gwamnati ta taimaka masu da tsaro su zauna a gidajensu cikin rufin asiri, wahalar da suke ciki ta yi yawa.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA da ta jiha SEMA a bayanin da suka fitar a jiha sun ce sun san da zaman 'yan gudun hijirar da suka gudu kan matsalar 'yan bindiga.
Bayanin ya ce "a karamar hukumar Shagari daruruwan mutane sun bar muhallan su kan rashin tsaron da ya Kunno Kai a yankin suna neman dauki.
"Don ganin halin da ake ciki Hukumomin sun tafi rukunin gidaje 30 a karamar hukumar in da mutanen suka zauna sun tuntubi hakimman mutanen daga cikinsu akwai hakimin ‘Yan Dundaji, Malam Muhammad Bello Magaji, da Maigarin Tungar-Barke, Muhammadu Tudu, wanda ya tabbatar da harin da aka kai musu kwana uku baya, yana da 'yan gudun hijira da yawa."
Sauran kauyukkan da abin ya shafa sun hada da Tungar-Barke, Lungu, Aske-Dodo, Tungar-Doruwa, Zango, ‘Yan Yandu, Tungar Na’anza, Ila, da sauransu.
A halin da ake ciki hukumomin na kira ga gwammati ta kawo daukin gaggawa musamman samar da tsaro a kauyukkan don mutanen su koma gidajensu cikin aminci.
Wakilinmu ya tuntubi shugaban karamar hukumar Shagari Honarabul Alhaji Maidawa sai dai bai samu jin ta bakinsa ba har zuwa hada labarin.