Mutane Da Dama Sun Mutu Yayin da Fada Ya Kaure Tsakanin Hausawa Da Fulani a Sokoto

Mutane Da Dama Sun Mutu Yayin da Fada Ya Kaure Tsakanin Hausawa Da Fulani a Sokoto

 

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an samu tashin hankali a garin Gwadabawa da ke jihar Sokoto, bayan wani rikici ya kaure tsakanin Fulani da Hausawa a yankin. 

Mummunan karon ya yi sanadiyar mutuwar mazauna yankin da dama daga bangarorin biyu, ciki harda jami'an tsaro na soja. 
Wani jami'in yankin, Aminu Gwadabawa, ya fadama VOA Hausa a wata hira da ta yi da shi a ranar Asabar cewa mutane na zaman dar-dar a yankin, yayin da rikicin ya yi sanadiyar mutuwar wani soja. 
"Suna tsoron hare-haren ramuwar gayya daga yan bindigar Fulani." 
A cewar wani da ya tsallake rijiya da baya: "Fulani sun farmaki dan uwana da wukake. Amma yana da wani kafiya da ba zai tar abu mai tsini ya shiga jikinsa ba. 
"Don haka sai suka ci gaba da kai masa hari sannan suka yi nasarar fille kansa daga jikinsa." 
Hakazalika, wani Bafulatani da ya tsira daga rikicin ya ba da nashi labarin. A cewarsa: "Sau biyu aka harbe ni amma na tsira. Na roke su da kada su kashe ni. Amma sai suka harbe ni." 
VOA Hausa ta rahoto cewa da aka tuntubi 'yan sandan jihar Sokoto, sun ce har yanzu suna jiran cikakken bayani kan harin.