Mutane 7 sun rasu a gobarar da ta tashi a gidan mai a Jigawa
Rundunar Tsaron Fararen hula ta Ƙasa, NSCDC, ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai a wata gobara da ta tashi a wani gidan mai dake Al-Masfa dake Ƙaramar Hukumar Kaugama a Jihar Jigawa.
Jami’in hulda da jama’a na NSCDC a Jigawa, Adamu Shehu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a Dutse a yau Talata, ya shaidawa manema labarai cewa lamarin ya faru ne a jiya Litinin da misalin karfe 5 na yamma.
“Gobarar ta kone gini da ke ɗauke da ofisoshi da kuma wurin kwana g'na ma’aikatan gidan man.
“Abin takaici, wasu daga cikin wadanda abin ya shafa na barci yayin da wasu ke hutawa.
"Sakamakon haka, shida daga cikin wadanda abin ya shafa sun mutu nan take yayin da daya ya cika bayan an kai shi asibiti."
Shehu ya bayyana cewa sai da a ka yi taron dangi jami’an kwana-kwana da jami’an tsaro wajen kashe wutar da ta rura sosai, wanda har yanzu ba a gano musabbabin tashin ta ba.
Ya bayyana sunayen mamatan da Nasiru Umar mai shekaru 30; Abdulkadir Nura, 25; Dahawi Garin-Babale 35; Hamza Adamu, 15; Sulaiman Garin-Babale, 35; Idris Adamu mai shekaru 40; da Salisu Garin-Babale, 40.
managarciya