Mutane 29 Sun Rasu Bayan jirgin Ruwa Ya Rabu Biyu a Sakkwato
Tsohon mataimakin gwamnan Sakkwato Barista Mukhtari Shagari ya aika sakon ta'aziya rasuwar mutanen tare da rokon Allah ya gafarta masu ya kare aukuwar hadarin a gaba. "ina yi wa mai girma gwamna da mutanen Sakkwato ta'aziyar wannan rashin Allah ya garta."
Jirgin ruwan kwale-kwale ya nutse da wasu matasa 33 a kauyen Gidan Magana a karamar hukumar Shagari ta jihar Sakkwato abin da ya yi sanadiyar rasuwar mutum 29 nan take.
Jirgin ruwan ya dauke su ne za su je daji domin samar da itacen girki da sauran wasu bukatu a wasu kauyukkan na kusa da su ya hadu da wani busasshen iccen Giginya abin da ya sanya ya rabu gida biyu matasan maza da mata suka nutse a ruwan.
Kansilan mazabar Bilyaminu Abubakar Ginga a lokacin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga Aminiya ya ce a halin da ake ciki mutanen gari sun yi kokarin aikin gayya in da suka samu nasarar dauko gawa 29 ta matasan da suka shiga cikin jirgin in da a yanzu bayan Azahar ana neman sauran, mace 23 da namiji 6.
"jirgin yana daukar mutum 32 zuwa da 33, matasa ne a cikinsa daga bakin shekara 16 zuwa kasa, suna kan haya ne jirgin ya samu hadari a sanadiyar bugun icce da ya yi a cikin ruwan, ya dauke su ne sufuri domin a kaisu wasu kauyukka makwabta da karfe 10 na safen Laraba lamarin ya faru da su," a cewar Kansila.
Honarabul Alhaji Maidawa Kajiji dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Shagari a majalisar dokokin jiha ya ce mutane 29 ne suka rasa rayukkansu a cikin jirgin kuma an yi masu sutura kamar yadda addini ya tanada.
"ko a shekarar data gabata an samu irin wannan hadarin kusan shekara uku kenan a jere ana samun salwantar rayuwa a ruwan nan sai dai a koyaushe yanayin rasuwar yana bambanta.
"wannan jirgin da ya tuntsure sanadin bugun busasshen icce dake kasan ruwa, na zamani ne da wani ya saya domin yin kasuwanci a yankin hakan ya sa muka daukar wannan abu ne daga Allah," a cewar Maidawa kajiji.
Ya yi kira ga gwamnatin jiha ta hada hannu da gwamnatin tarayya domin samar da babbar gada a saman gulbin wanda hakan zai sa a tsiratar da rayuwar mutanen yankin domin ba su da wata hanya da suke mu'amala da junansu sai an tsallaka ruwan.
Tsohon mataimakin gwamnan Sakkwato Barista Mukhtari Shagari ya aika sakon ta'aziya rasuwar mutanen tare da rokon Allah ya gafarta masu ya kare aukuwar hadarin a gaba.
"ina yi wa mai girma gwamna da mutanen Sakkwato ta'aziyar wannan rashin Allah ya garta."
managarciya