Mutane 12 sun mutu a kauyen Gada-Biyu da ke kan titin Abuja zuwa Lokoja bayan wata tirela mai ɗauke da gawayi ta buge mutane da ke tsaye a gefen hanya.
Hatsarin ya haɗa da, motar Sharon mai kujeru 18 da kuma Motoci 2 kirar Volkswagen Golf, wadanda suka mutu akwai Maza manya 4 , mata manya 2 da yara maza 4 da kuma yara mata 2.
An kai waɗanda suka jikkata asibitin Abaji, inda direban tirela da mai taimaka masa suka tsere.
A Kaduna, Mutane 10 sun mutu a hanyar Kachia zuwa Jaba sakamakon fashewar taya da ta haddasa hatsari tsakanin motoci biyu a garin Kwaturu.
Mutane 17 hatsarin ya rutsa dasu gaba ɗaya, biyar aka ceto inda aka Kai su asibiti, inda ɗaya ya rasu daga bisani.
Hatsarin ya faru ne dalilin Ggdun wuce kima da tukin ganganci da kuma fashewar taya
Hukumar FRSC ta ce tana ci gaba da daukar mataki kan irin wadannan haɗurra.






