Muna Kira Ga Buhari Ya Kori Ministan Shari'a Abubakar Malami---Isah Achida

Muna Kira Ga Buhari Ya Kori Ministan Shari'a Abubakar Malami---Isah Achida

Shugaban jam'iyar APC na jihar Sakkwato Alhaji Isah Sadik Achida  masu biyayya ga Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kori ministan shari'a Abubakar Malami kan kujerarsa domin bai dace ya ci gaba da riƙa kujerar ba.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a taron manema labarai da ya kira a ofis na jam'iya a jihar Sakkwato, ya ce cire shi yakamata a yi domin abin da ya yi na shiga gaban kotu bai dace ba ga wanda yake riƙe da kujerar doka a tarayyar Nijeriya.
Haka ma ya roƙi minista Malami da ya yi murabus don ya bayyana cewa shi mutum ne da bai kamata ya riƙe ofishin lauyan gwamnatin tarayya ba.
 Achida ya ce uwar jam'iyya APC ta ƙasa yakamata ita ma ta takawa Malami birki a ƙoƙarinsa na tarwatsa APC  a jihohin Kebbi da Zamfara da Kwara da Sakkwato da sauran wurare.
Achida ya ce maganar Malami na kiran wani ɓangare shugabanni bayan magana na gaban kotu bai kamata ba, wannan shiga gaban kotu ne kuma shi ba kotu ba ne.