Mun yabawa hukuncin Kotu kan kujerar ɗan majalisar waƙillai-----Shugaban APGA
Jam'iyyar APGA Ya Yabawa Hukuncin Kotu Kan Kujerar Majalisar Wakilai
An bayyana cewar yanzu kotu ce kadai talakan kasar nan yake tinkaho da ita wajen karban hakkinsa. Shugaban jam'iyyar APGA a jihar Neja, Malam Musa Aliyu Liman ne ya bayyana hakan bayan hukuncin kotu kan takaddamar jam'iyyar PDP na kin amincewa da kayen da ta sha a lokacin zaben cike gurbi na dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Rijau da Magama.
Tunda farko dai dan takarar kujerar majalisar a karkashin jam'iyyar PDP, Hon. Emmanuel Alamu ne ya shigar da karar kin amincewa sakamakon zaben Hon. Shehu Sale Slow na jam'iyyar APGA. Inda a satin da ya gabata kotun sauraren karar zabe ta sake tantance sakamakon tare da tabbatar wa Shehu Slow wannan kujerar.
Da yake bayyana farin cikinsa kan wannan hukuncin, shugaban jam'iyyar yace APGA jam'iyyar siyasa ce ta kasa ba yanki ko wasu kabilun jama'a, ban yi mamakin yadda al'ummar Magama/Rijau suka baiwa Hon. Shehu Slow kuri'a ba, domin hakan na nuna cewar sannan a hankali talakawa sun fara dawo wa daga rakiyar jam'iyya ko gishiri da omon da ake ba su a lokacin zabe, jam'iyyar APGA ba ta da kudi amma a jihar Taraba muna da dan majalisar da yanzu haka zuwan shi majalisar tarayya na uku ke nan.
Hon. Shehu Sale Slow ya tafi majalisar a inuwar APC, bayan ya dawo jam'iyyar APGA yau kuma ya sake komawa, wannan na nuna cewar zuwan sa na farko ya taka rawar ganin da jama'a suka gamsu da shi ke nan. Idan ka dubi zabukan 2015 ya bambanta da na 2019, haka na ke kyautata zaton 2023 ma zai zo da salon wayewa da cigaba.
Duk wanda ke tunanin cewar APGA jam'iyyar wani bangare ne na kasar nan, to lallai ya jahilci dokar qasa, domin ba dokar da ta amince da kafa jam'iyya dan wani bangare, kan haka ne APGA ke da kundin tsare tsare da ya dace da dokokin kasar nan. Saboda haka 'yan siyasa su daina saurin shiga jam'iyyu masu karfi ko masu rike da madafun iko, ya zama na sune karfin jam'iyya ta hanyar kyautatawa jama'a.
Ba mu yi mamaki ba, idan ka dubi yadda aka gudanar da zaben nan da kuma yadda zaben yazo, al'umma ne suka yi zaben kuma suka tsare kayan su, har Allah ya tabbatar da wannan hukuncin, musamman kutunan da mu ke da su kotuna ne masu gaskiya domin da su ne talaka ya dogara.
Ina jawo hankalin Hon. Shehu Sale Slow ya bi manufofin jam'iyyar APGA sau da kafa domin manufofi ne na inganta rayuwar al'umma, wanda idan ya cigaba da yadda ya faro da yardar Allah jam'iyyar APGA za ta kawo karshen bangar siyasa a jihar nan, bangar siyasar nan itace ta jefa kasar nan a halin rashin tsaron da mu ke fuskanta a kasar nan.
Shugaban ya shawarci gwamnati tarayya da ta fadada dubarun ta kan matsalar tsaron da ya addabali kasar nan, a tarihin duniya kasar Italiya ta taba yin zarra a garkuwa da mutane dan karban kudin fansa, yau wannan ya zama tarihi, dan haka ina shawartar gwamnatin tarayya da ta nemo masana masu kishi dan kawo karshen wannan matsalar da ke kokarin gurgunta kasar nan.
managarciya