Mukhtar Shagari Ya Bar  PDP Bayan Shekaru 24 Yana Cikinta

Mukhtar Shagari Ya Bar  PDP Bayan Shekaru 24 Yana Cikinta

Mukhtar Shagari Ya Bar  PDP Bayan Shekaru 24 Yana Cikinta

 Tsohon ministan albarkatun ruwa, Alhaji Mukhtar Shehu Shagari ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP bayan shekara 24 yana cikinta. Tsohon mataimakin gwamnan na jihar Sokoto, Shagari ya yi murabus daga jam'iyyar PDP kuma ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC). 
Ya bayyana hakan ne a turakarsa ta twitter ya nuna ya bar jam'iyar tafiyar tasa ba ta zo da mamaki ba ganin yanda ya yi yunkurin fita a farkon kakar zaben 2023 bayan da bai samu tikitin takarar Gwamna  ba.