Mu ne Halastattun Zaɓaɓɓun Shugabannin APC A Sakkwato----Injiniya Aminu Ganda
Gaskiyar magana ba darewa gida biyu a jam’iyar APC ta jihar Sakkwato ta yi ba, sai dai akwai jayayya wadda ita ce ake yi, a lokacin da aka yi zabe uwar jam’iyya ta turo kwamitin da aka baiwa hakkin yin zabe sun zo wurinmu aka tara daligate bayan gudanar da zabe sun kai sakamako a wurin uwar jam’iya mu ne halastattun zababbun shugabannin jam’iya duk da akwai masu ganin su ne suka yi ruwa da tsaki a cikin jam’iyya har kullum suna ganin jam’iyya ta su ce, sun mai da ta kamar wani shago, ba su yarda da samun canjin shugabanci ba.
Managarciya ta zanta da daya daga cikin jigogi jam’iyar APC a Sakkwato kan sha’anin jam’iyarsu da harkar tsaro a jihar Sakkwato.
Za mu so ka gabatar da kanka
Sunana Injiniya Aminu Ganda zababben Sakataren APC a Sakkwato, Kwamishina a hukumar da shugaban kasa ya samar domin taimakawa mutanen da ke kusa ga korama da ruwa ke yi wa barna a gefen Kebbi da Neja Filato don samar da hanyar taimaka masu da samar musu da matsugunni.
Wane hali APC take ciki kan zaɓen shugabanni da aka gudanar
Gaskiyar magana ba darewa gida biyu a jam’iyar APC ta jihar Sakkwato ta yi ba, sai dai akwai jayayya wadda ita ce ake yi, a lokacin da aka yi zabe uwar jam’iyya ta turo kwamitin da aka baiwa hakkin yin zabe sun zo wurinmu aka tara daligate bayan gudanar da zabe sun kai sakamako a wurin uwar jam’iya mu ne halastattun zababbun shugabannin jam’iya duk da akwai masu ganin su ne suka yi ruwa da tsaki a cikin jam’iyya har kullum suna ganin jam’iyya ta su ce, sun mai da ta kamar wani shago, ba su yarda da samun canjin shugabanci ba.
Abubuwan da suka kawo tsaikon rantsar da shugabanni a jiha biyu ne zuwa uku da ake iya ciwo kansu, uwar jam’iya tanason rantsar da shugabanninta gaba daya a jihohi 36 hakan ya sa ake jiran jihohin da ba su yi zabe ba su kammala.
APC za ta iya cin zaɓe a 2023 a Sakkwato?
Jam’iyar PDP dake mulki a Sakkwato sun kusa kammala shekara bakwai a mulki mutane sun ga abin da ke faruwa da ganin bambanci dasauran jihohi, in ka duba nan kusa kasuwa ta kone an kasa gyara ta, duba a cikin gari ina sheda maka cewa duk Nijeriya Sakkwato ita ce tafi kazanta, kwasar shara ma abin ya gagara balle nemowa mutane aikin yi abubuwa sun tabarbare, da ikon Allah za mu tsayar da ‘yan takara sanannu da za mu ci zabe a 2023.
Duk da rabuwar kai a APC za ku ci zaɓe?
Sanata Wamakko Sarkin Yamma uba ne ga jam’iyar APC dukanmu na shi ne, a 2019 in baka manta ba an yi jayayya bayan kammala zaben fitar da gwani aka dawo tare domin abu guda ake, ita siyasa a kullum ta gadi jayayya akwai ta cikin gida duk wanda Allah ya baiwa sai a dawo a bi shi, mu mun dauka ko da Sanata Wamakko bai da sha’awa da mu uba ne gare mu, bayan an rantsar da shugabanmu za mu tafi wurinsa godiya kuma za mu yi masa biyayya, da ikon Allah mun san zai ba mu goyon baya a dunke baraka a yi tafiya guda.
Matsalolin da aka samu a baya wanda ya sanya APC ta rasa kujerar gwamna za a yi kokari a baiwa wannan matsalar baya a tabbatar da samun kujerar gwamna a 2023.
Mi zaka ce kan matsalar tsaron gabascin Sakkwato
Matsalar tsaro a gabascin Sakkwato abu ne da ke baiwa kowa takaici domin maharan ana iya maganinsu da ikon Allah, za a yi amfani da jami’an tsaro don magance matsalar ina iya tunawa Bafarawa ya ba mu labari an taba samun irin haka ya bi dare ya je Abuja ya yi mitin da wasu shugabannin tsaro aka ba shi ‘yan sandan sirri a cikin asiri aka yi kacakaca da miyagun ba wanda ya sani kuma tun daga lokacin ba wanda ya ji duriyarsu, muna da yakini in an zauna abu ne da ake iya maganinsa amma an sanya siyasa a ciki baka jin wani yunkuri da gwamna ke yi sai dai ganin laifin gwamnatin tarayya alhali gwamna ke da hakki na farko kan magance lamarin in gwamna ya tafi da na shi jadawali kan hanyar da za a bi a kawowa jiharsa zaman lafiya shugaban kasa ba zai ki aminta ba, ya samu shugabannin tsaro da jadawalinsa mana, da akwai shugabanci nagartacce a Sakkwato da wannan lamarin bai kazanta ba, sakakaci ne na gwamnatin Sakkwato ya kada gabascin Sakkwato cikin halin rashin tsaro.
managarciya