Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna.
An bayyana cewar hukuncin kotu kan rikicin APC a Sokoto babban nasara ce, domin an kawo taƙaddamar rikicin cikin gida da muka fuskanta a baya. Jigo a jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Gudu, Malam Murtala Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wakilin mu a minna fadar gwamnatin Neja.
Malamin ya cigaba da cewar babu wani ɗan siyasar da ya baiwa jam'iyyar APC gudunmawa a jihar nan kamar Sanata Aliyu Wamakko, dukkanin masu taƙaddamar ba wanda bai anfani Sanata Wamakko ba, abinda suka yi na jayayya akan shugabancin jam'iyya ba su yi laifi ba, domin wannan na nuna APC ta samu karɓuwa kuma jama'a sun gamsu da jagorancinta.
Ya kamata tunda kotu ta kawo ƙarshen taƙaddamar, lokaci yayi da za mu goyi bayan waɗanda suka samu nasarar dan tunkarar babban zaɓen da ke gaban mu.
Malam Murtala, ya cigaba da cewar mun fuskanci matsalar tsaro a jihar Sokoto na ƴan bindiga da ƙungiyar ISIS, wanda kusan ya ɗaiɗaita al'amurra, duk da haka ina jawo hankalin mutanen karkara da su daure su tafi dan yiwa yaran da suka kai wa'adin jefa ƙuri'a da su tabbatar sun mallaki katin zaɓen su dan samun damar yin zaɓe a zaɓuka masu zuwa.
Rashin mallakar katin zaɓe zai hana waɗanda suka cancanci jefa ƙuri'a damar zaɓen mutanen da suka dace. Domin akwai buƙatar kowani ɗan Nijeriya yayi zaɓe a babban zaɓe mai zuwa domin sauke haƙƙin da ke kan sa da zai ba shi damar mutanen da yake kyautata zaton zasu ba shi wakilcin da ya kamata.
Wajibi ne shugabanni su tashi tsaye wajen wayar da kan mutane muhimmancin wannan katin zaɓen musamman yaran da ba su samu damar mallakar katin ba a baya da waɗanda suka samu canjin matsugunnai sakamakon tashe-tashen hankulan ƴan ta'adda.
Malamin ya cigaba da cewar maganar zaɓen shugabannin jam'iyya a matakin ƙasa, kar mu yarda mu raba kawunan mu, mu tabbatar mun goyi bayan dukkan wanda Allah ya baiwa shugabancin jam'iyyar dan samar da tsarin dimukuraɗiyya mai inganci.