Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Sokoto ta Arewa Honarabul Abdullahi Hassan ya ƙalubalanci hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC kan gayyatar da take yi wa tsofaffin gwamnonin Arewa.
Abdullahi Hassan na ganin hukumar ba ta kiran takwarorin gwamnonin da suka fito daga Kudancin Nijeriya, kan haka yake tambaya mi ya sa haka?
A baya bayan nan hukumar ta gayyaci tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasir Elrufa’i in da zai halarta a ranar Litinin mai zuwa lamarin da ‘yan siyasar ke kallo da bita da ƙullin siyasa.






