Mi Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Don Raba Sakkwato Da Daukar Kofin Talauci A Nijeriya?

Mi Ya Kamata Gwamnati Ta Yi Don Raba Sakkwato Da Daukar Kofin Talauci A Nijeriya?

 

Gwamnatin tarayya da hukumar kididdigar kasa NBS ta saki rahoton adadin mutanen dake cikin bakin talauci a kasar a shekarar 2022. 

NBS a sabon rahoton da ta fitar ranar 17 ga Nuwamba. 

Ta bayyana cewa kashi 63 na dukkan ‘yan Najeriya suna cikin matsanancin talauci tare da fatara. 
Hakan na nufin mutum miliyan 133 ne ke cikin bakin talauci na rashin abinci, kiwon lafiya, aikinyi, ilimi, da sauransu.
A fadin Najeriya gaba daya, Jihar Sokoto ce tafi yawan Talakawa, bisa jadawalin TheCableIndex.
Sokoto mai dauke da  Mutum Milyan 5.8,  kashi  90.5% na fama da talauci.
Bisa jadawalin, mutum kashi 9.5% na al'ummar jihar Sokoto ne kadai suke ci su koshi lafiya kulli yaumin.  

A matsayinka na mutum mai hankali mi kake ganin ya kamata gwamnati ta yi don raba Sakkwato da daukar kofin talauci a Nijeriya?