MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Shida

Yana gama typing text din ya tura fiskarsa dauke da murmushi bakinsa na furta kalmar ina matukar kaunarki Amal  murmushi ya kuma yi kafin ya tsunduma cikin kogin tinanin kanwar tasa wacce ya reni soyayyarta tin tana karama kawo wannan lokacin, yaja dan guntun tsaki mtsww! Kafin ya ce ai ita har yanzu batama san da zaman soyayyan da nake mata ba, tinda har yanzu bata wani girma sosai ba, yadan bata fiska kafin yace ya zama dole na samo mafita dangane da wannan soyayyar, ya daga hannu sama yana mai cewa " YA ALLAH INA MAI ROKONKA KA KAWOMIN KYAKKYAWAR MAFITA CIKIN WANNAN MAKAUNIYAR  SOYAYYAR DA NAKE  YI" Yana gama fadin hakan yace Ameeeeen sannan ya shafa hannayesa bisa fiskarsa.

MEE'AD Labarin Soyayya Mai Rikitarwa:Fita Ta Shida
          _*MEE'AD*_
                  
Lttafin  HAUWA IBRAHIM MISAU
 
 
               
 
                   13 --14
 
Ranar sunday 9 o clock bakidayansu sun shirya tsaff dan raka Yaya Majeed filin jirgi, yayin da baki dayan iyayensu suka shiga moto 1,  Majeed, Mee'ad da Amal suka shiga moto daya drive yana driving cike da kwarewa.
 
Majeed ya dago kai fiskarsa dauke da murmushi yana fadin Amal idan na tafi zamu rinka waya ko? Amal ta dan tabe fiska kafin tace haba yaya wani waya zamu rinqa yi kuma? Ni kam bani wani son yawan wayan nan gaskiya, 
 
"Majeed ya danyi jimm kafin ya ce ki yi hakuri ko a wayar Umma muna gaisawa kin ji Kanwata? 
 
Amal ta gyara zama kafin ta ce haba yaya dan tsabar rashin kunya sai mu rinka yin waya da kai ta wayar Umma? Gaskiya ba lallai na iya hakan ba," 
 
Murmushi Majeed yayi kafin ya ce idan ba mu yi waya da wayar Umma ba da wayar wa za mu yi?"
 
"Mee'ad dake gefen Amal zaune sai kallon titi take sai a lokacin ta tanka musu cikin hikima take fadin Yaya duk wannan abin ba wani abun daga hankali ba ne a iya tinanin gaskiya  a shawarce mi zai hana tin da ina da system kuma da simcard a ciki sai ku rinka chat kawai tanan kunga ba wanda zai ma san mike tafiya a tsakani koba haka ba? 
 
Majeed yayi murmushin jin dadi kafin ya riko hannun Mee'ad yace love u much Kawata  gaskiya kina da basira sosai, daga yau kin zama kawata kin ji? Murmushi Mee'ad ta yi kafin ta ci gaba da kallon titi tana mai duba time cikin agogon dake daure bisa hannunta, Majeed yadan gyara zama kafin ya ce Kanwata kin yadda zamu rinka yin chat dake? Eh Amal ta ce tana mai yatsina fiska  murmushi Majeed yayi kafin ya ci gaba da danna wayar dake hannun sa.
 
"Ba wanda ya karayi magana a cikinsu har suka isa airport, jiran 'yan mintina suka yi kafin jirginsu Majeed ya tashi, suka juyo gida cike da kewarsa dan kuma 'yan 2 har kuka suka yi da yake sun fara wayo sosai.
 
"Majeed ya sauka a masukin sa gwanin sha'awa 'a kasar India, bayan yayi wanka yaci abinci ya kwanta bisa katafaren gadon dake shimfide a dakin, ya dan yi shiru kadan ba abinda yake tinani sai gida da kuma yan kannensa daya bari suna kuka, murmushi yayi a lokacin da zuciyarsa ta tina masa da Amal cikin zumudi ya dauko system dinsa ya kunna cikin kankanin lokaci ya fara typing message kamar haka...
 
"" Kanwata na iso cikin farin ciki , kuma kasar india kasa ce mai kyan gaske tare da abubuwa masu kayatarwa, akwai dukkan abinda nake bukata, amma nayi kewar gida bakin daya musamman ke, gaskiya nayi miss dinki sosai  kuma zan so ace ki kularmin da kanki ako wani irin lokaci ki ce ina gaishe da Mee'ad babbar kawata, ki kuma gaida su Umma".
 
Yana gama typing text din ya tura fiskarsa dauke da murmushi bakinsa na furta kalmar ina matukar kaunarki Amal  murmushi ya kuma yi kafin ya tsunduma cikin kogin tinanin kanwar tasa wacce ya reni soyayyarta tin tana karama kawo wannan lokacin, yaja dan guntun tsaki mtsww! Kafin ya ce ai ita har yanzu batama san da zaman soyayyan da nake mata ba, tinda har yanzu bata wani girma sosai ba, yadan bata fiska kafin yace ya zama dole na samo mafita dangane da wannan soyayyar, ya daga hannu sama yana mai cewa " YA ALLAH INA MAI ROKONKA KA KAWOMIN KYAKKYAWAR MAFITA CIKIN WANNAN MAKAUNIYAR  SOYAYYAR DA NAKE  YI" Yana gama fadin hakan yace Ameeeeen sannan ya shafa hannayesa bisa fiskarsa.
 
A can Nijeriya kuma Mee'ad kwance take bisa kan gado tana danna system dinta sbd tana matukar son karatu ko danna system a ko wani irin yanayi,  wannan dalilin yasa Daddy ya sai mata system din,  ita kuma Amal tace tafison mp shiyasa Daddy ya sai mata mp mai kyau da tsada, " Mee'ad tana kan danna system dinta yayin da Amal ke gaban dress mirrow tana kwalliya," 
 
"Mee'ad ta dubi Amal fiskarta dauke da murmushi kafin tace 6ter albishirinki?"
 
Murmushi Amal tayi kafin tace goro fari tass "
 
"Mee'ad ta gyara zama kafin tace yayanki ya tura miki sako yanzu, ki zo ki karanta tabe baki Amal tayi kafin tace ki karanta dai inajinki Mee'ad ta bude ta fara karantawa kamar yadda ya rubuta tana cikin Karan tawar,  Amal tace ke kin ga kyaleni da wannan karatun kin ji? Mee'ad ta ce wai ke Amal mike damun ki ne? Amal ta kara tabe fiska kafin tace kinga tafiyata sai ki yi ta karanta wannan shirmen zancen idan kin gama saiki masa reply tana gama fadin haka tayi ficewarta abinta, jijjiga kai Mee'ad ta yi kafin tace Allah ya shirya min ke Amal, ta danyi jim kafin taci gaba da karanta text din da Yayan nasu ya turo tana murmushi.
 
              
 
             ---------------------------------
 
 
 
 
Bayan Mee'ad ta gama karanta text din ta yi masa reply kamar haka..
 
"Ina fatan ka isa cikin koshin lpy? Duk dama jikina yana bani hakan dafatan kaci abinci kum kayi wanka kamar yadda ka saba a kullum? Dukkan mutanen gida suna lpy,  sai dai kewanka da ya hana kowa sukuni. Ka ji dadin kasar India Yayana daga Kanwarka Mee'ad. 
 
"Sai da ta rubuta sunanta tayi wani tinani saita goge ta mayar da sunan Yayarta ta kamar haka " daga Kanwarka Amal". 
 
Ta yi murmushi kafin ta tura masa text din ba tare da tinanin komai ba," bayan ta tura taci gaba da danne2 ta cike da kwarewa.
 
Washe gari suna idar da sallan asuba suka fara shirin tafiya skull Mee'ad ta rika Amal shiyawa harta fita harabar gidan sai kuma ta dawo dakin nasu da gudu tana fadin na yi mantuwa" 
 
"Hararar ta Amal ta yi kafin ta ce ubanmi kuma kika manta murmushi Mee'ad ta yi kafin tace na manta ido nane bari ma kiga na dauko shi,"
 
"Ta sunkuya ta bude murfin site drower ta rungumo system dinta tana dariya take fadin to kinga idon nawa dana manta din ko 
 
"Tsaki Amal taja kafin tace dalla bani waje mashirmaciyar banza kawai computer ne zaki wani kira shi da sunan ido?"
 
" Mee'ad ta kara kyalkyalewa da daria kafin ta sanya system dinta cikin jaka ta nufi kofar fita da gudu tana fadin idan ba kiyi sauri ba zamu tafi mu barki sai ki biyo bus, 
 
Amal ta tabe baki kafin ta rufa mata baya da gudu tana fadin bazanyi saurin ba kuma nafi karfin nabi bus tinda Umma ma ta fadamin haka.
 
"Mee'ad kara gudu tana fadin kanki akeji ai.
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
Pls fans don't forget to read, vote & share to other groups.
 
 
 
 
Love u much my fans.
 
 
Pls 
 
Fans
 
Ku
 
Nemeni 
 
Akan
 
Wannan 
 
No din
 
 
Dan ba da shawara ko makamancinta, haka zalika idan kina/kana son shiga MEE'AD FANS GROUP dukanku nemeni ta wannan no din 09039285813 
 
 
 
 
 
 
 
Taku har kullum Hauwancy Misau.