MEE'AD LABARIN SOYAYYA MAI RIKITARWA:FITA TA SHA TARA

MEE'AD LABARIN SOYAYYA MAI RIKITARWA:FITA TA SHA TARA


          MEE'AD
                   
             
              Cigaban Littafi  

     

         
      
 Pls don't forget to vote, share & comments  love u fan's.
           


Ina kuke masu son DATA? ku taho da hazanri ku saya dan kuma nazo muku da Data a sassaukan rahusa idan kuna bukata

    MTN

50MB ₦50
150M ₦100
250MB ₦110
500MB ₦50
1GB      ₦250
1.5GB ₦400 
2GB     ₦500

2.5GB ₦650 
3GB     ₦750 
3.5GB   ₦900
4GB    ₦1000
5GB  ₦1250
6GB   ₦1500 
10GB. ₦2500
15GB. ₦3800
20GB. ₦5000

Mai bukata ya tura ta wannan account number

3142669195 Hauwa Ibrahim First Bank .

Idan ka tura saika tuntubeni ta wannan number

09039285813.

Ga masu bukata akwai Glo da Airtel da kuma 9mobile.

Masu bukatar katina kowani layima akwai a kasa.

Maza kuzo kada 'a barku a baya sbd ga dama ta zo muku har cikin gida.

41 ~ 42


'Kura mata ido yayi sannan yace Umma kina nema nane ? eh tace kanta 'a duke" murmushi yayi ya wuce ta gefenta yana cewa Mommy sai na dawo.

Cike da kunya Umma ta nufi dakinta, zama tayi bisa gado tana tinanin abinda ya faru rintse idanu tayi, jingina jikinta tayi bisa gado tana mai mutukar jin haushin kanta.

"Waya ta dauka tayi kiran Aunty Safiyya" Assalamu alaikum yar uwata dafatan shirin mu ya kammala" ? murmushin yake Umma tayi hmm ina kuma shiri ya kammala, kinsan ma miya faru ? yau naji kunyar daban taba tsammanin zanji ba 'a rayuwata" nan ta fada mata dukkan abinda ya faru." 

Daria Safiyya tayi sannan tace haba Auntyna nikam banga wani abin jin kunya 'anan wajen ba" dan kawai Sirikinki ya ganki sai kuma ki sare ? gaskiya ki koyi dakewa ' a kowani irin yanayi. nifa karki sanyani jin kunya.

Dogon ajiyar zuciya Hajiya suwaiba taja bazaki ra'ba gane mi nake son cewa ba Safiya dan haka 'abar zancen kawai. Amma yanzu miye abinyi ?

Daria Safiyan ta karayi hmm kinsan mi zakiyi yanzu kuma ? jijjiga kai tayi bata ce komai ba. yayinda Safiya taci gaba da cewa inaso ki manta da wani abu ya shiga tsakaninki da yaron nan, kawai ki tinkari hanyar dana dauraki akayi wancan lokacin.

Shiru Umma tayi jiki a sanyaye ta amsa mata da too, sannan sukayi sallama, shiru da tinane ~ tinane sune suka biyo bayan sallaman da sukayi.


%%%%%


Mee"ad ce zaune bisa kujerar falon Hajiya, Tv ne kunne amma kana ganin fuskarta kasan hankalinta ba 'akan kallon yake ba.

Hajiya ce ta shigo falon hannunta ri'ke da plas, hango Mee'ad tayi zaune a falo fuskarta cike da mamaki ta karasa wajen da take zaune tana fadin 'a'a yau manyan bakine a gidan namu ? isowar yaushe ?

Murmushi tayi gamida gyara zama hmm Hajiya kenan dama nayi tsammanin bakisan da zuwana ba shiyasa ban tasheki daga bacci ba.

"Kai amma naji dadin zuwanki kinga zan tambayi Usman daya barminke a kiyi sati daya sai sbd mu huta sosai.

"Dakin burgeni kuma! kiga sai mu zauna mu rakashe abinmu.
Daria sosai Hajiya Hindu tayi kinga kuma jibi y'an uwanki zasuje sallama kinsan sunyi kusa wucewa " kuma gashi akwai biki a gidan Alhaji Malam makwotan mu sbd jiya sun tambaya wai amaren anan zasu zauna damin suna tinanin gidan bazai ishesu ba.

Murmushi tayi sannan ta ce Hajiya kenan mai jama'a Allah yaa kaimu lokacin. Kuma idan har Daddy ya 'amince na zauna tare dake sai kinyi mini anko.

Dolena nayima takwarata anko sbd baniso ta fito daban cikin jerin y'an matan biki.

Daria sosai Mee'ad tayi tuni dukkan 'bacin rai da tazo dashi ya kauce fira kawai sukesha cike da kulawa.

Amal yau da wuri ta tashi daga school kai tsaye gidansu Amrah suka wuce sbd sunfi samun sakewa 'acan din.

Mee'ad na hango cikin kitchen girki take hannunta rike da ludayi yayida Hajiya Hindu ke zaune a gefenta hira suke suna daria " Hajiya ce take cewa haka kika iya girkin tsofi ? tukunna ma waya koya miki naga waccar sakaryar ko ruwan zafi bata iya dorawa 'a gas ba.

Daria tayi haba hajiya! miyasa kike son cin fuskar y'ar uwatace nikam banison hakan gaskiya! ta karasa maganar fuskarta ' a shagwa'be.

Murmushi Hajiyar tayi a'a su masu y'ar uwa to maida wukar bazan kara ta'ba miki y'ar uwar taki ba. baki fadamin waya koya miki girki haka ba"

Gyara tsayuwa tayi kafin tace Hajiya kenan ko kin manta da Mom bafulatana ce kuma fulanin daji, ga kuma Daddy da Abba suma jinin fulanine ke gudana cikin jikinsu, idan kuma baki manta ba akwai ranar da kike bani labari akan yanda 'ake koya muku girki tin kuna yara, to ninafi tsammanin iya girkin da nayi na gadone daga dukkan 'bangare guda biyu.

Kuncinta Hajiya taja sannan tace kinada wayo sosai Allah yayi miki albarka.

"Ameen Hajiyata!   

Kiran wayarta Majeed yayi amma batai picking ba. Tsaki yaja mtswww! yaci gabada driving.

Parking yayi a harabar gidan ya fito daga mota fuskarsa dauke da murmushi ya nufi cikin gidan.

Zaune ya tarar dasu bisa darning" da sallama ya shiga yana fadin Hajiya ina Kawartawa take ? ya karaso cikin falon fuskarsa dauke da murmushi.

Hajiya Hindu ta dubeshi cike da mamaki ta ce sai yau kaga daman zuwa gidan Amaryar taka ? to maraba ya hanya ka karaso kaci girkin Kanwar taka.

"Murmushi yayi ya ce a kawomin abincin falo anan zanci"

"Murmushi Mee'ad tayi yaya an wuni lafiya" ? 

"Hararar wasa yayi, ina kuma lfy bayan kin taho gidan Hajiya baki sanar dani ba"

"Murmushi tayi Allah ya huci  zuciyarka Yayana tuba nake,"

"Shikenan ya wuce, mi kuka dafane haka ? shiru tayi batace komai ba.

Hajiya ta ce abincin gargajiya tayi mana yau barina kawo maka  kaji kota iya girki"

Nasan Mee'ad gwanace wajen iya girki, kawo na ta'ba naji. Zama yayi kan rool carpet din dake shimfid'e a falon.

'Diban abincin tayi ta nufi sama tana cewa kaga nikam nayi nan zanje nayi wanka Mee'ad ta zuba maka 'abincin.

Binta da kallo yayi harta 'bace. dawo da kallonsa kan Mee'ad yayi ya ce kinga kawomin abincin dama yunwa nakeji, murmushi tayi kafunta debo abincin.

Zama tayi a gefensa 'ajiye flat da cups d'in dake hannunta tayi bismillah Yaya ga 'abincin. Ok zauna muci ko Kawallita"

'Bata fuska tayi wacece Kawallin taka "

"Murmushi yayi ina wata bayanke" zauna muci tare kawai sbd nan ba gida bane dan naga 'alamar a gida bakya ta'ba sakewa.

Murmushi tayi kafin ta zauna to muci abincin ko ? hannu yasa suka fara cin abincin tare fira suke suna daria.

Amal tana gidansu Amrah zaune sai zance sukeyi suna shewa! Umma ce ta kirata take shaida mata Majeed yabi Mee'ad gidan Hajiya" Kan uban can! yabi wama kikace to wllh bai isaba katse wayar tayi, figi gyalenta tana cewa ke tashi ki rakani gidan Hajiya"

Wai Majeed ya tafi gidan Hajiya wajen Mee'ad shewa! Amrah ta buga sannan ta ce dama mi nake fad'a miki akan waccar kod'ad'd'iyar tashi muje...


pls 

Follow 

Share

Vote

Comment

Fisabilillah.