Mazauna rukunin gidaje na Yauri Plats BQ dake Sokoto sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna adawa da matakin gwamnatin jihar.
An ga gomman mazauna Yauri Plats a ranar Talata suna zanga zanga kan korarsu daga rukunin gidajen da gwamnatin jihar ta yi bayan ta yi masu alkawalin za a sayar masu da gidajen.
Masu zanga-zangar, sun mamaye sakatariyar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen Sakkwato dauke da kwalaye da rubuce-rubuce daban-daban inji rahoton Daily Trust.
Masu zanga-zangar dai sun yi zargin cewa korarsu daga gidajen da suka shafe sama da shekaru 40 suna zama a ciki ba daidai ba ne.
An tattaro cewa akalla dakuna 180 kowanne mai dauke da akalla mutane shida ne gwamnatin jihar Sokoto ta sanyawa alamar rusawa a rukunin gidaje na Yauri Plats.
Mazauna gidajen da abin ya shafa da suka hada da mata da yara na kwana a filin Allah kusa da rukunin gidajen tun bayan korar da aka yi musu a makon jiya.
Talatu Yusuf, daya daga cikin mutanen da aka haifa kuma suka girma a rukunin gidajen, ta shaida wa Aminiya cewa tun a 1992 iyayenta ke zama a gidan.
“An kore mu a makon da ya gabata kuma a halin yanzu, ba mu da wani matsugunni.
Tun makon da ya gabata muke kwana a filin Allah.” – A cewar Talatu.
Wata mata mai suna Malama Aisha Bala ta ce ta shafe shekara 21 a gidan da take ciki, ta ce an tilasta musu kwana a kan titi bayan korar su.
