Mazauan Rukunan Gidajen Gwamnati Sun Nuna Rashin Gamsuwa da hukuncin Gwamnatin Sakkwato

Mazauan Rukunan Gidajen Gwamnati Sun Nuna Rashin Gamsuwa da hukuncin Gwamnatin Sakkwato

 

Mazauna rukunin gidaje na Yauri Plats BQ dake Sokoto sun gudanar da zanga zangar lumana domin nuna adawa da matakin gwamnatin jihar. 

An ga gomman mazauna Yauri Plats a ranar Talata suna zanga zanga kan korarsu daga rukunin gidajen da gwamnatin jihar ta yi bayan ta yi masu alkawalin za a sayar masu da gidajen.
Masu zanga-zangar, sun mamaye sakatariyar kungiyar 'yan jarida ta Najeriya reshen Sakkwato  dauke da kwalaye da rubuce-rubuce daban-daban inji rahoton Daily Trust. 
Masu zanga-zangar dai sun yi zargin cewa korarsu daga gidajen da suka shafe sama da shekaru 40 suna zama a ciki ba daidai ba ne. 
An tattaro cewa akalla dakuna 180 kowanne mai dauke da akalla mutane shida ne gwamnatin jihar Sokoto ta sanyawa alamar rusawa a rukunin gidaje na Yauri Plats. 
Mazauna gidajen da abin ya shafa da suka hada da mata da yara na kwana a filin Allah kusa da rukunin gidajen tun bayan korar da aka yi musu a makon jiya.
Talatu Yusuf, daya daga cikin mutanen da aka haifa kuma suka girma a rukunin gidajen, ta shaida wa Aminiya cewa tun a 1992 iyayenta ke zama a gidan.
“An kore mu a makon da ya gabata kuma a halin yanzu, ba mu da wani matsugunni. 
Tun makon da ya gabata muke kwana a filin Allah.” - A cewar Talatu. 
Wata mata mai suna Malama Aisha Bala ta ce ta shafe shekara 21 a gidan da take ciki, ta ce an tilasta musu kwana a kan titi bayan korar su.