matsalar  tsaro na cigaba da ta'azzara a arewacin Nijeriya

matsalar  tsaro na cigaba da ta'azzara a arewacin Nijeriya
 
Daga Abbakar Aleeyu Anache.
 
'Yan Najeriya sun fusata kan yadda lamarin tsaro ke tabarbarewa a arewacin kasar.
 
Al’umman Najeriya sun fusata suna nuna fishi kan abun da suka kira gazawan jami’an tsaro kan yadda lamarin satan mutane ana garkuwa dasu yake kara ta'azzara.
 
Abin da ya kara tunzura jama’a shine na baya-bayan nan da aka yi a yankin Bwari na garin Abuja babban birnin kasar inda aka kwashi iyalan gida daya kuma ake ta kashe su a duk sanda ranar kawo kudin fansa ya zagayo ba’a cika wa’adi ba.