Home Labarai Matsalar tsaro: Ministan tsaro da  Sarkin Zuru sun gana a Abuja

Matsalar tsaro: Ministan tsaro da  Sarkin Zuru sun gana a Abuja

11
0

Ministan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Zuru Alhaji Sanusi Mikailu Sami Sami Gomo III tare da rakiyar tawagarsa  a ofishinsa dake babban birnin tarayya Abuja inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi a rashin tsaro a yankin Zuru da jihar Kebbi.

Ganawar ta samu halartar dan majalisar wakilai mai wakiltar masarautar Zuru Hon Kabir Ibrahim Tukura Gamjin Zuru da sauran yan’ majalisar Sarki ciki hadda General Ishaya Bamaiyi Maj Gen Muhammadu Magoro Galadiman Zuru.

Rahotanni sun nuna cewa ziyarar ta mayar da hankali ne kan karfafa sha’anin tsaro tare da katse ayyukan yan ta’addan da suka addabi masarautar Zuru da jihar Kebbi.

A cikin wata sanarwa da Abbakar Aleeyu Anache ya fitar ta bayyana ganawar tana da nasaba da inganta sha’anin tsaron masarautar.

Abbakar Aleeyu Anache

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here