Matsalar Tsaro: Gwamna Lawal Ya Ba Da Tabbacin Tura Jami’an Tsaro Zuwa Kauyukan Zamfara 

Matsalar Tsaro: Gwamna Lawal Ya Ba Da Tabbacin Tura Jami’an Tsaro Zuwa Kauyukan Zamfara 

 

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi alkawarin taimakawa iyalan wadanda aka kashe a hare-hare kan kauyukan Janbako da Sakkida da ke karamar hukumar Maradun ta jihar. 

Lawal ya yi alkawarin ne lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya da jaje ga garuruwan da abun ya shafa. 
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Malam Mani Malam Mumini, ya ce gwamnatinsa na aiki tukuru don magance yawan hare-hare a jihar. 
Ya ce gwamnatin jihar na tsara hanyoyin da za a bi wajen taimaka wa marasa galihu da ma al’ummomin da suka yi fama da matsalar yan fashi da barayin shanu na tsawon shekaru. Darakta Janar na labaran jihar, Malam Nuhu Salihu Anka, ya ce gwamnatin jihar na shirya jerin sunayen mutanen da miyagun kusa kashe don taimaka masu. 
"Gwamnatin ta bayar da gudunmawar naira miliyan 2 ga iyalan da abun ya shafa kuma jami'ai za su fara aiki nan ba da jimawa ba don ganin yawan barnar da maharan suka yi sannan su shirya tsari mai kyau na saukaka wahalar da mutanen ke ciki.