MATSALAR TSARO A arewacin Najeriya an kama jami'in shige da fice da safarar manyan makamai ga yan ta'adda

MATSALAR TSARO A arewacin Najeriya an kama jami'in shige da fice da safarar manyan makamai ga yan ta'adda
Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta cafke wani tsohon jami’in shige da fice da ke yunkurin sayar da manyan bindigogi ga ‘yan bindiga da ke aiki a dazuzzukan Abuja-Kaduna.
Jami’in da aka kora, wanda ba a bayyana sunansa ba, an kama shi ne bayan wani samame da hukumar ‘yan sanda ta kai.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Larabar da ta gabata, jami’in da ke kula da sashin yaki da masu garkuwa da mutane, Mustafa Mohammed, ya ce farmakin ya hana makaman kaiwa ga masu aikata laifuka,
Mohammed ya ce, “A bisa bayanan sirri, rundunar ta kama wadannan bindigogi daga korarriyar jami’in shige-da-fice da ke yunkurin sayar da su ga ‘yan fashi da ke addabar dajin Abuja-Kaduna. An samu bayanan sirri cikin lokaci, kuma an kama makamai a lokacin da yake kokarin kai kayan.
Mohammed ya ce daga cikin makaman da aka kwato akwai Scorpion CZ EVO3, wani nagartaccen makami mai sarrafa kansa.
Daga Abbakar Aleeyu Anache