Matashi Ya Sanar Da El-rufa'i Sha’awarsa Ta Son Tsayawa Takarar Gwamnan  Kaduna

Matashi Ya Sanar Da El-rufa'i Sha’awarsa Ta Son Tsayawa Takarar Gwamnan  Kaduna

Daga Ibrahim Hamisu.


Fitaccen matashin nan daga dan jihar Kaduna Muntaka Abdulhadi Dabo, ya sanar da sha’awarsa ta son tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna a kakar zabe mai zuwa ta  2023.

Muntaka wanda ake yi wa laƙabi da “Sardaunan Abari Ya Huce” ya sanar da hakan ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-rufai, wacce jaridar MANAGARCIYA ta samu kwafi.

Sai dai a cikin wasiƙar bai shaida jam’iyyar da zai tsaya takarar ba.

Matashin dai sanannen ɗan kasuwa ne kuma masanin fasahar sadarwa. Shi ne shugaban ƙungiyar tsoffin ɗaliban buɗaɗɗiyar jami’ar Najeriya wato (National Open University of Nigeria Alumni Accociation, NOUNAA).

Haifaffen jihar Kaduna ne da ya fito daga ƙaramar hukumar Zaria.

Ko a shekarar 2019, matashin ya fita neman tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar ta Kaduna sai dai ba a kai ga zaben fiɗɗa gwani ba ya janye.

Muntaka ya kasance memba a kwamitin yaƙin neman zaben shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a zaben 2019.

Muntaƙa Dabo wanda tsohon maaikacin tuƙin jirgin sama na Midview ne. Sannan ya taɓa rike  shugabancin Ƙungiyar Gizago social and Cultural Association ne har karo biyu, ya kasance matashi kuma dan gwagwarmaya da ya je kokarin fade gaskiya jikin dacinta.