Matasa masu kishin tafiyar siyasar tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa sun nemi da ya dawo harkar siyasa gadan-gadan bayan ya sanar da jingine siyasa da ya yi a lokuttan da suka gabata.
Matasan da suka taru a gidan Bafarawa don su roke shi ya sake dawowa cikin harkokin siyasa ba kamar yadda ya kudurta a farko ba, sun ce siyasar Sakkwato ba ta inganta in ya cire hannunsa cikinta.
Alhaji Babangida amadadin matasa ya zayyano muhimmanci Bafarawa a siyasar Sakkwato Wanda hakan zai sa su magoya bayansa ba za su lamunce ya cire hannunsa a harkokin siyasa ba.
Tsohon Gwamna Bafarawa a jawabin da ya yi wa magoya bayansa kan bukatar su, ya sanar yanda yake rayuwa tun bayan barin mulki a cikin dogara da Allah hakan yake so magoya bayansa su kasance komai abarwa Allah, amma dai a tashi a yi aiki don cigaba a jihar Sakkwato.
In ba a manta ba tsohon Gwamnan ya sanar cewa ya yi ritaya a siyasa abin da ya haifar da cece ku ce a jiha ganin wannan maganar wani abu ne mai wahalar gaske tsohon Gwamna ya jingine siyasa.





