Wasu matasa ɗauke da muggan makamai sun tare wasu manyan motocin bus masu daukar mutum 18 a hanyar Jos zuwa Zaria inda suka auka musu nan take suka kashe akalla mutum sama da 20, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Daily Nigerian wanda ta ce wakilinta ya ziyarci wannan wuri bayan wannan mummunar abu ya auku na rashin imani da rajanta bil'adama.
Ya ce matafiyan na dawowa daga taron murnar shiga sabuwar shekarar musulunci da aka yi a garin Bauchi bisa gayyatar Sheikh Dahiru Bauchi, kamar yadda Ibrahim wanda ya tsira daga wannan hari ya bayyana ka kenan dukkan wadanda aka kashen muslmai ne.
Majiyar ta bayyana cewa koda motocin suka isa gada-biyu dake karamar hukumar Jos ta Arewa sai matasan suka dirar musu, suka fara sara suna duka.
"Mutum fiye da 80 sun arce cikin daji. Sannan kuma na ga wasu gawarwaki har 22 waɗanda na ƙirga da kai na a asibitin koyarwa na jami’ar Jos." kamar yadda yake fadi.
Hanyar garin Jos tana fama da wadannan bata garin 'yan ta'adan sunkuru dake labewa suna cutar da mutane masu shiga garin ko fita.
Ko a watannin baya sun tare hanyar in da suka kashe wani Dan jijar Kebbi dake aiki a Abuja in da ya bar matarsa daya da 'ya'ya uku.
Akwai matukar bukatar hukumomi su kara daukar matakin kan wannan hanyar da sauran wuraren bata gari ke labewa domin cutar da mutane abin da ke kai da rasa rayuwa.